Yobe: Ƙaburbura 650 sun rufta sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye makabarta

Yobe: Ƙaburbura 650 sun rufta sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye makabarta

  • Ambaliyar ruwa da ya faru bayan ruwan sama ya janyo kaburbura sun rufta a garin Gashua da ke jihar Yobe
  • Wasu mazauna garin sun ce a kalla kaburbura 650 ne suka rufta sakamakon ambaliyar da ya mamaye wurare da dama a garin
  • Mazauna garin sun yi kokarin bude hanyoyin ruwa domin saukaka lamarin amma duk da haka sun nemi a kai musu dauki

A kalla kaburbura 650 ne suka rufta a babban makabartar garin Gashua da ke karamar hukumar Bade a jihar Yobe sakamakon ambaliyar ruwa da ya mamaye wasu yankunan garin.

Daily Trust ta ruwaito cewa ambaliyar ruwan ya mamaye makabartar ne bayan ruwan sama da aka yi a ranar Asabar.

Yobe: Ƙaburbura 650 sun rufta sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye makabarta
Kaburbura 650 sun rufta yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye makabarta a Yobe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Abinda mutanen gari suka ce game da ambaliyar ruwan

Daily Trust ta ruwaito cewa wani shaidan gani da ido, Idris Anthony Brah, wanda ya ziyarci makabartar ya nuna damuwa matuka game da abin da ya faru.

Ya ce:

"Kaburbura da dama sun rufta kuma ana iya ganin wasu gawarwakin da aka birne, wanda hakan ya tilastawa mazauna garin yin tururuwa zuwa makabartar.
"Mun dauki kayayyakin aikin mu mun haka hanyoyin ruwa saboda mu rage ruwan da ya taru a makabartar kada ya lalata sauran kaburburan."

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Wani mazaunin garin mai suna Yahaya Mato, ya ce lamarin ya fi karfinsu don haka sun dai iya abin da za su iya wurin rage ruwan da ke kwance a makabartar.

Mato ya ce wasu sassan katangar da aka zagaye makabartar ya rushe.

Ya yi kira ga gwamnati da mutane masu hali su taimaka domin a gyara kaburburan.

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

A wani labarin daban, kun ji cewa ana zaman dar-dar a cocin Dunamis da ke Lugbe Abuja bayan yan sanda da wasu jami'an tsaro masu farin kaya sun zagaye yankin da cocin ya ke saboda tsoron yiwuwar kutsen mambobin #Revolutionnow da ke zanga-zangar kama wasu mambobinsu da DSS suka yi, The Guardian ta ruwaito.

A yayin da The Guardian ta ziyarci cocin a safiyar ranar Lahadi, ta gano yan sanda da dama a yankin, yayin da motoccin sintiri kimanin guda hudu sun tsaya a wasu muhimman wurare a unguwar.

Mai rajjin kare hakkin bil-adama da goyon bayan demokradiyya, Omoyele Sowore, ya yi barazanar sake yin wata gagaruman zanga-zanga idan ba a sako mutane biyar da aka kama sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' ba a ranar Lahadi da ta gabata a cocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel