Daga ƙarshe, an kama wanda ya kitsa kisar gillar da aka yi wa Shugaba Moise

Daga ƙarshe, an kama wanda ya kitsa kisar gillar da aka yi wa Shugaba Moise

  • Yan sanda a kasar Haiti sun ce sun kama wanda ya kitsa kashe Shugaba Jovenel Moise
  • Wanda aka kama wani likita ne mai shekau 63 mazaunin Amurka amma dan asalin kasar Haiti
  • Rundunar yan sandan Haiti ta ce wadanda ake zargin suka aikata kisan sun kira shi a waya bayan kisan kuma an samu wasu hujjoji a gidansa

Rundunar yan sandan kasar Haiti, a ranar Lahadi ta sanar da kama mutumin da ake zargin shi ya kitsa yadda aka kashe Shugaba Jovenel Moise, The Punch ta ruwaito.

Wani likita dan Haiti mazaunin jihar Florida a kasar Amurka ne ake zargi da kitsa kisar a cewar shugaban yan sanda Leon Charles a wani taron manema labarai.

Daga ƙarshe, an kama wanda ya kitsa kisar gillar da aka yi wa Shugaba Moise
Shugaba Jovenel Moise na kasar Haiti. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Wadanda ake zargin su suka aikata kisar sun kira shi a waya bayan harin sannan an gano abubuwa da ke nuna yana da hannu a kisar a gidansa, in ji Charles.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

Premium Times ta ruwaito cewa likitan mai shekaru 63 ya iso kasar ta Haiti a yan kwanakin nan cikin wani jirgi na musamman domin ya kwace shugabancin kasar a cewarsa.

Ya yi hayar makisa na kasar Columbia ta hanyar wani kamfani mai zaman kansa na tsaro da ke Florida.

Likitan shine mazaunin Amurka na uku dan asalin kasar Haiti - kuma mutum na 21 - da aka kama kuma ake tsare da shi a matsayin wanda ake zargi da hannu cikin kisar.

Sauran wadanda ake zargin biyu suma mazauna jihar Florida ne.

Jihar ta Florida na da nisar kilomita 1,000 daga kasar Haiti.

Yan sanda sun ce makasa na haya yan kasar Columbia 26 ne suke da hannu a kisar baki daya, an kashe uku, 18 suna tsare sannan yan sanda na neman sauran guda biyar.

Manyan jami'an Amurka da ake sa ran za su taimaka a binciken sun gana da Charles a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka sace shugaban wata kwaleji a jihar Zamfara

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Yadda aka kashe Moise

An harbe Moise mai shekaru 53 ne a gidansa da ke Port-au-Prince a safiyar ranar Laraba. An yiwa matarsa Martine mugun rauni inda daga bisani aka kaita Florida don yi mata magani.

Kawo yanzu ba a tabbatar da dalilin kisar ba.

Moise ba shi da farin jini a kasar tun hawansa mulki a 2017. Ana zarginsa da rashawa, alaka da kungiyoyi masu hatsari da yiwuwar sauyawa zuwa mai mulkin kama karya.

An dade ana fafatawa kan mulki a kasar na Haiti

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

A wani labarin daban, kun ji cewa ana zaman dar-dar a cocin Dunamis da ke Lugbe Abuja bayan yan sanda da wasu jami'an tsaro masu farin kaya sun zagaye yankin da cocin ya ke saboda tsoron yiwuwar kutsen mambobin #Revolutionnow da ke zanga-zangar kama wasu mambobinsu da DSS suka yi, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Aikin Kwangila: Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi

A yayin da The Guardian ta ziyarci cocin a safiyar ranar Lahadi, ta gano yan sanda da dama a yankin, yayin da motoccin sintiri kimanin guda hudu sun tsaya a wasu muhimman wurare a unguwar.

Mai rajjin kare hakkin bil-adama da goyon bayan demokradiyya, Omoyele Sowore, ya yi barazanar sake yin wata gagaruman zanga-zanga idan ba a sako mutane biyar da aka kama sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' ba a ranar Lahadi da ta gabata a cocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel