Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru

Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru

  • A ranar Lahadi ne miyagun 'yan bindiga suka shiga fadar sarkin Kajuru suka yi awon gaba da shi
  • Kamar yadda matar basaraken ta sanar, sun shiga dauke da miyagun makamai sanye da kayan sojoji
  • Harin yafi kama da shiryayye domin sai da suka rufe duk wata hanyar shige da fice kuma suka yi musayar wuta da sojoji

Kajuru, Kaduna

Bayanai na cigaba da bayyana kan harin da aka kai masarautar Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kutsa fadar basaraken inda suka yi awon gaba da shi tare da iyalansa 13.

Garin Kajuru yana da nisan kilomita 37 daga birnin Kaduna. Garin yana nan a babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia kuma yana da iyaka da Chikun ta Kujama inda aka sace dalibai 121 na makarantar Bethel Batist a ranar Litinin da ta gabata.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga

Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru
Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

A ranar Lahadi, miyagun 'yan bindiga masu tarin yawa sun mamaye garin Kajuru a abinda mazauna garin suka fassara da shiryayyen hari.

"Sun kai farmakin tsakanin karfe 12 zuwa 2 na dare, sun rufe duk wata hanyar shige da fice na tsohon garin kafin su shiga gidan basaraken," ganau ya sanar da Daily Trust.

Mazauna garin sun fada dimuwa bayan harin

Kamar yadda aka gano, a yayin da 'yan bindigan suka tsinkayi gidan basaraken da na 'yan uwansa dake kusa da fadar, sun mamaye wurin sojojin dake kallon GSS Kajuru kuma suka dinga musayar wuta na tsawon sa'a daya.

'Yan uwan basaraken sun sanar da cewa 'yan bindigan sun samu shiga gidan basaraken ta wata hanya karama.

'Yan bindigan sun balle babbar hanyar daga baya inda suka shiga tsakar masarautar inda basaraken yake da matansa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

Matar basaraken ta biyu, Hadiza Alhassan ta ce 'yan bindigan sun banko dakinta inda suka daka mata tsawa ta sanar dasu inda basaraken yake yayin da sauran suka fasa kofar.

'Yan bindiga dauke suke da bindigogi, sanye da kayan sojoji

Ta ce, "Dauke suke da makamai miyagu kuma sanye suke da kayan sojoji. Na sanar dasu cewa sarki baya nan, daya daga cikinsu yace zan yi bayani idan suka gan shi yayin da suka cigaba da kokarin fasa kofar dakinsa.

"Lokacin da suka yi nasara, sun cire kofar kuma suka shige dakin. Sun fito dashi sannan suka tambaya ko shi ne basaraken kuma ya amsa da eh, hakan yasa suka yi gaba da shi."

A wani labari na daban, mukabalar da aka dade ana jira tsakanin Sheikh Abduljabbar da sauran malaman Kano ta kare da rigima domin an kasa tsayawa a tsayayyar matsaya.

Bayan kammala mukabalar, Daily Trust ta gano cewa an shirya mika malamin gaban kotu kan laifukan batanci. 'Yan sanda sun mika takarda domin ya bayyana a gaban hedkwatar 'yan sanda a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka sace shugaban wata kwaleji a jihar Zamfara

Wata majiya makusanciya da malamin ta sanar da Daily Trust cewa tuni dama an shirya wadannan zargin kan Abduljabbar wanda aka shirya dauka daga wurin mukabalar wacce aka yi a hukumar Shari'a ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel