Cikakken Bayani: An sanar da ranar fara taron gangamin jam'iyyar APC

Cikakken Bayani: An sanar da ranar fara taron gangamin jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC mai mulkin kasa ta ce za ta fara gangamin taronta na bana a ranar 31 ga watan Yuli
  • Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na APC ne ya sanar da hakan ciki wasikar da ya aike wa INEC
  • Kamar yadda ya ke a cikin wasikar za a fara tarurukan ne a matakan mazabu sannan, sai kananan hukumomi sannan jihohi

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa ta tsayar da ranar 31 ga watan Yulin 2021 domin fara gangamin tarurukanta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da farko, jam'iyyar ta dage yin tarurukan har sai masha Allah wanda hakan ya haifar da cece-kuce.

An sanar da ranar fara taron gangamin jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC za ta fara gangaminta a ranar 31 ga watan Yuli. Hoto: The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

Amma cikin wata wasika mai kwanan wata na 11 ga watan Yuli, Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC da Sanata John James Akpanudoedehe, sakataren jam'iyyar sun sanar da sabon ranar fara tarurukan.

Kara karanta wannan

Kotu ta sanar da ranan sauraran karar da PDP ta shigar kan sauya shekar gwamna Matwalle

A wasikar da suka aike wa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, sun ce za a fara tarurukan ne a mazabu sannan kananan hukumomi kafin jihohi su biyo baya, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

A cewar jadawalin da aka direktan tsare-tsare na jam'iyyar APC, Farfesa Al-Mustapha Ussiju Medane, ya fitar da farko, za a fara sayar da tikitin takara na mazabu daga ranar 1 ga watan Yuli zuwa 7 ga wata Yulin 2021.

Zamfara: Ba za mu bari abin da ya faru da APC a 2019 ya sake faruwa ba, Yeriman Bakura

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma mai neman takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Sani Yerima, ya ce masu ruwa da tsaki a siyasar jihar za su haɗa kai don ganin ba a maimaita abin da ya faru a 2019 ba, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Kotun koli ta soke kuri'un APC a zaben 2019 a jihar Zamfara don jam'iyyar bata da ikon tsayar da ƴan takara don bata yi zaben fidda gwani ba yadda ya dace.

A hirar da ya yi da manema labarai a karshen mako a Abuja, Yerima ya ce babu rikici a jam'iyyar APC ta Zamfara kan shigowar Gwamna Bello Matawalle cikin jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel