Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

  • Iyayen daliban da yan bindiga suka sace daga FGC Birnin Yauri a jihar Kebbi sun ce yan bindiga sun aurar da yaransu
  • Wasu daga cikin iyayen sun ce yan bindigan sun turo musu faifan bidiyo inda suka ce tuni sun aurar da yaransu
  • Hakan na zuwa ne kimanin makonni biyu da yan bindigan suka sace daliban a makarantarsu kuma har yanzu ba a ceto su ba

Iyayen ɗalibai mata da aka sace daga makarantar sakandare ta gwamnatin tarayya da ke Yawuri, jihar Kebbi, suna neman taimako, suna mai cewa an aurar da ƴaƴansu, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar wasu daga cikin iyayen yaran, masu garkuwa da mutanen sun rika tura musu faifan bidiyo da ke nuna cewa sun riga sun aurar da yaransu.

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Da Aka Sace a Kebbi Sun Koka
Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Da Aka Sace a Kebbi Sun Koka
Asali: Original

DUBA WANNAN: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Daily Trust ta ruwaito cewa yanzu kimanin makonni biyu kenan bayan da aka sace daliban daga makarantarsu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka sace shugaban wata kwaleji a jihar Zamfara

Daya daga cikin iyayen daliban ya shaidawa BBC Hausa cewa a duk lokacin da suka kira mas garkuwar, su kan fada musu cewa yaran na cikin koshin lafiya.

Da gwamnati muke son tattaunawa ba da ku ba

Amma, masu garkuwar suna fada musu cewa ba da su suke son yin magana ba, da gwamnati suke son yin maganan kudin fansar.

Ya ce:

"Wasu lokutan sukan kira su hada mu da yaran mu muyi magana. Idan yar ka nada lambar ka, za su kira ka yi magana da su, amma ni banyi magana da 'ya ta ba tun lokacin da aka sace su."

Ya kara da cewa tun da aka sace su, yara 10 ne kadai cikinsu suka kira suka yi magana da iyayensu.

KU KARANTA: Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari

Ya ce wasu daga cikin iyayen sun yi taro da gwamnatin jihar Kebbi a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

Ya ce:

"Gwamna ya nuna damuwarsa kan lamarin kuma ya ce zai dauki mataki, yau kimanin sati biyu kenan amma ba mu ji komai ba."

Ya kara da cewa a yanzu suna rayuwa ne cikin fargaba a yayin da Sallah ke gabatowa.

"Kowa na zaune cikin farin cik a gidansa, amma muna rayuwa cikin zullumi."

Ya bukaci gwamnati ta taimaka ta ceto yaransu daga hannun wadanda suke tsare da su domin su samu kwanciyar hankali.

El-Rufai ya bayyana dalilin cire yaronsa daga makarantar gwamnati

A wani labarin, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana dalilin da yasa ya cire yaronsa mai shekaru bakwai, Al-Sadiq El-Rufai daga makarantar Kaduna Capital School a sirrance, Daily Trust ta ruwaito.

A shekarar da ta gabata ne gwamnan ya saka dansa a makarantar ta gwamnati amma daga bisani rahotanni suka nuna ya cire shi.

A hirar da aka yi da shi da BBC Pidgin, El-Rufai ya ce yan bindiga na bibiyan dansa ne suyi garkuwa da shi saboda matakin da ya dauka ne dena biyan kudin fansa.

Kara karanta wannan

Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel