Yadda PDP Ta Mulki Jihohi 31 Shekaru 14 da Suka Gabata da Yadda APC ta Kwacesu

Yadda PDP Ta Mulki Jihohi 31 Shekaru 14 da Suka Gabata da Yadda APC ta Kwacesu

Tsokacin Edita: Bayan da gwamnan jihar Zamfara, da wasu 'yan majalisu da dama suka bayyana ficewarsu daga jam'iyyar PDP, kafafen sada da na watsa labarai sun cika da martani daga magoya bayan jam'iyyar PDP, dama kanta jam'iyyar ta PDP. A bangare guda, ta bayyana cewa, ba ta damu da sauya shekar tasu ba, yayin da a wasu rahotanni kuwa jam'iyyar ta bayyana cewa, za ta iya kwace kujerar gwamnan jihar Zamfara. Sai dai, wannan ba sabon abu bane, domin jam'iyyar PDP ta taba kasancewa jam'iyyar da ta mamaye jihohin Najeriya, wanda a yanzu aka samu sauyi.

A ranar Talata, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya koma jam'iyyar APC a hukumance. An zabi Matawalle ne a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Punch ta ruwaito.

Lamarin sauya shekar gwamna Matawalle ya jawo cece-kuce, inda jam'iyyar PDP ta zargi jam'iyyar APC da zawarcin gwamnonin PDP a boye tare da yi tsorata domin shiga jam'iyyar da karfi, jaridar Punch ta tattaro.

Sai dai, jam'iyyar PDP ba karamar jam'iyya bace da bata saba mulki a Najeriya ba, akalla, ta yi mulkin shekaru 16 kafin wata jam'iyya ta karba a Najeriya.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa

Waiwaye: Yawan Jihohin da PDP Ta Mulka a Cikin Shekaru 14 da Suka Gabata
Kididdigar yawan jihohin da APC da PDP ke mulki | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A shekarar 2007, PDP ta yi mulki a duk fadin kasar kuma ta yi alfahari da cewa ita ce "jam'iyya mafi girma a Afirka". Ta kuma yi alfaharin cewa za ta mulki kasar na tsawon shekaru 60, in ji jaridar TheCable.

Ya zuwa ranar 30 ga Mayun 2007, PDP tana da jihohi 31 a karkashin ikonta.

Jihohin sun hada da Abia, Adamawa, Anambra, Akwa Ibom, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Ribers, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Yayin da rusasshiyar jam'iyyar ANPP ke da jihohin Yobe, Kano, Bauchi, da Borno, ita kuma rusasshiyar jam'iyyar AC tana da Legas.

Kotu daga baya ta tsige Andy Uba na PDP a matsayin gwamnan jihar Anambra, kuma wannan ya share fagen fitowar Peter Obi wanda ke dan jam'iyyar APGA ne a lokacin.

A yanzu APC ce mai rike da yawan jihohin Najeriya

Sai dai, a yanzu idan aka koma baya ga sauyin shekar da aka yi, a halin yanzu jam'iyyar APC ce ke rike da mafi yawan jihohin kasar.

Jam’iyyar mai mulki tana da jihohi 22, jam'iyyar adawa ta PDP na da jihohi 13 yayin da APGA ke rike da jiha daya tak.

A yanzu haka, jihohi 13 da ke karkashin babbar jam’iyyar adawar (PDP) sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Benue, Delta, Edo, Enugu, Oyo, Ribas, Sokoto da Taraba.

APC, a daya bangaren, tana rike da Borno, Cross River, Ebonyi, Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Plateau, Yobe da baya-bayan nan Zamfara.

Zaben gwamnan Anambra da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba zai nuna ko PDP za ta iya dawo da asarar da ta yi ta hanyar karbe jihar daga APGA.

KARANTA WANNAN: Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC

Yawan ku Ba Zai Hana Mu Karbar Mulki a 2023 Ba, PDP Ta Caccaki Gwamnonin APC

A wani rahoton na daban, Jam’iyyar PDP ta ce ba ta damu da sauya shekar da gwamnoni a karkashin jam’iyyar suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba, tana mai cewa tana da kyakkyawan shiri na karbe kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Gwamna Bello Mattawalle na jihar Zamfara a hukumance ya koma APC daga PDP a ranar Talata, ya zama gwamna na biyu da ya bar babbar jam’iyyar adawar zuwa jam’iyya mai mulki bayan wata daya kacal da takwaransa na jihar Kuros Riba Ben Ayade ya koma APC.

Amma PDP ta nace cewa ficewar ba wani abin damuwa ba ne, tana mai cewa APC ba ta cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya ba, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel