PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa

PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana matakin da za ta dauka idan gwamnan Matawalle ya yarda ya sauya sheka zuwa APC
  • A cewar PDP, kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba shi damar ficewa daga jam'iyyar da aka zabe shi ba zuwa wata
  • Ta ce lallai yana wasa da kujerararsa ne idan ya kuskura ya sauya sheka zuwa APC dashi da sauran 'yan majalisu

Gabanin shirin sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP, zuwa APC, babbar jam'iyyar adawar (PDP) ta gargadi gwamnan kan wannan matakin, tare da barazanar yin mai yiwuwa don kare dokokin jam'iyya.

PDP ta gargadi Bello Matawalle da ya sani cewa take-takensa sun yi daidai da shawarar barinsa kujerar mulki saboda an zabe shi a karkashin jam'iyyar PDP, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

Karshe PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Ficewar Gwamna Matawalle Daga Jam'iyyar Zuwa APC
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar PDP:

"Babu wata doka da ta ba shi damar tsallakewa zuwa wata jam’iyya tare da mukamin gwamna da aka ba PDP ta hanyar zabe, kamar yadda yake a Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma hukuncin Kotun Koli.”

Da yake magana da manema labarai a sakateriyar jam’iyyar jiya, kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya nuna rashin karbuwar yunkurin na gwamna Matawalle kamar yadda yake rubuce a kundin tsarin mulkin Najeriya da na hukumar zabe mai zaman kanta.

Wannan yasa PDP ta gargadi mambobin majalisar kasa daga jihar da kuma mambobin majalisar dokokin jihar ta Zamfara kada su yi wasa da kujerarsu ta hanyar sauya sheka zuwa wata jam'iyya wanda a cewar PDP hakan ya saba ka'ida, sai dai idan akwai rarrabuwar kawuna.

A nasa bangaren, Ologbondiyan ya bayyana karara cewa:

"Babu rarrabuwar kawuna a jam'iyyar PDP da zai bayar da kofar ficewar wani dan majalisar mu."

PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

Majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a gobe zai koma jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan yasa PDP ta ce za ta dauki matakin doka domin dakatar da gwamnan na Zamfara daga barin jam'iyyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba, an tattaro cewa za a ambaci karar da wasu jiga-jigan PDP suka shigar kan sauya shekar Matawalle a yau a kotu.

KU KARANTA: Obasanjo Ya Yi Gargadin Matsalar da Najeriya Za Ta Shiga Saboda Yawan Haihuwa

Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC

A wani labarin, Rahotanni sun tabbatar da cewa, gwamnan jihar Zamfara Matawalle zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC gobe.

A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar The Nation ya ce, mai magana da yawun gwamnan, Mista Yusuf Idris, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya cewa gwamnonin APC 18 za su yi maraba da shi.

Ya bayyana cewa:

"Yanzu an gama komai domin gwamnanmu ya sauya sheka daga PDP zuwa APC."

A cewarsa, gobe za a yi kasaitaccen liyafa a Gusau, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel