Yawan ku Ba Zai Hana Mu Karbar Mulki a 2023 Ba, PDP Ta Caccaki Gwamnonin APC
- Bayan da gwamnan jihar Zamfara ya koma jam'iyyar APC, PDP ta bayyana cewa ba ta ji haushin haka ba
- Ta ce dukkan gwamnonin da ke komawa APC su sani, PDP za ta karbi mulki a zaben shekarar 2023
- Ta kuma bayyana cewa, tsorone tsan-tsa ya sanya su komawa jam'iyyar APC saboda ana farautarsu
Jam’iyyar PDP ta ce ba ta damu da sauya shekar da gwamnoni a karkashin jam’iyyar suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba, tana mai cewa tana da kyakkyawan shiri na karbe kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Gwamna Bello Mattawalle na jihar Zamfara a hukumance ya koma APC daga PDP a ranar Talata, ya zama gwamna na biyu da ya bar babbar jam’iyyar adawar zuwa jam’iyya mai mulki bayan wata daya kacal da takwaransa na jihar Kuros Riba Ben Ayade ya koma APC.
Amma PDP ta nace cewa ficewar ba wani abin damuwa ba ne, tana mai cewa APC ba ta cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya ba, Channels Tv ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: Al’ajabi: Rafin da Mutane Masu Neman Haihuwa da Waraka Ke Zuwa Addu’a
Shugaban jam'iyyar ta PDP na kasa, Uche Secondus a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata ya bayyana cewa:
"Mun tsaya a nan ne don mu bayyana karara cewa za mu kafa gwamnati ta gaba a zaben 2023 saboda yawan jama'a, ba gwamnonin da ke barin PDP ba."
APC na farautar gwamnoni daga jam'iyyar PDP
Shugaban na PDP wanda ya zargi APC da “farautar gwamnoni” daga jam’iyyar tare da tsorata su don su shiga jam’iyyar mai mulki, ya bukaci APC da ta maida hankali kan dawo da tattalin arzikin kasar nan da kuma inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Shugaban na PDP yayin da yake kokawa da irin wahalar da ke tattare da al'ummar Najeriya, yace:
“Ban taba ganin kasar da kuke da matsalar tattalin arziki ba, da [rashin tsaro] sannan jam’iyya mai mulki za ta fara farautar gwamnoni… abin kunya ne ace duk gwamnonin sun sauya sheka saboda tsoro; sun tsorata da kayan aikin gwamnatin APC."
“Suna bin gwamnoninmu mu kuma za mu bi talakawan kasar nan, mutanen da ke shan wahala a karkashin wannan gwamnatin. Kuma wannan shi ne bambanci."
PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa
Gabanin shirin sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP, zuwa APC, babbar jam'iyyar adawar (PDP) ta gargadi gwamnan kan wannan matakin, tare da barazanar yin mai yiwuwa don kare dokokin jam'iyya.
PDP ta gargadi Bello Matawalle da ya sani cewa take-takensa sun yi daidai da shawarar barinsa kujerar mulki saboda an zabe shi a karkashin jam'iyyar PDP, jaridar Vanguard ta ruwaito.
A cewar PDP:
"Babu wata doka da ta ba shi damar tsallakewa zuwa wata jam’iyya tare da mukamin gwamna da aka ba PDP ta hanyar zabe, kamar yadda yake a Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma hukuncin Kotun Koli.”
KARANTA WANNAN: Rahotanni Sun Bayyana Yadda Aka Kamo Nnamdi Kanu a Wata Kasar Turai
A wani labarin, Rahotanni sun tabbatar da cewa, gwamnan jihar Zamfara Matawalle zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC gobe.
Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC
A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar The Nation ya ce, mai magana da yawun gwamnan, Mista Yusuf Idris, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya cewa gwamnonin APC 18 za su yi maraba da shi.
Ya bayyana cewa:
"Yanzu an gama komai domin gwamnanmu ya sauya sheka daga PDP zuwa APC."
A cewarsa, gobe za a yi kasaitaccen liyafa a Gusau, babban birnin jihar.
Asali: Legit.ng