Da duminsa: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Da duminsa: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

  • Dukkan masu mukaman siyasa a Zamfara sun sauya sheka APC illa mataimakin gwamna
  • Mataimakin ya bayyana dalilin da yasa ba zai bi maigidansa APC ba
  • Uwar jam'iyyar PDP ta lashi takobin kai Matawalle kotu

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Gusau, ya lashi takobin cewa zai cigaba da zama a jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, duk da cewa gwamnan jihar, Bello Matwalle ya koma All Progressives Congress APC.

Dukkan Sanatocin Zamfara uku, yan majalisar wakilai shida da yan majalisa jiha 24 sun sauya sheka tare da gwamnan illa mataimakinsa.

Muhammad Gusau ya ce zai cigaba da kasancewa da PDP saboda jama'ar PDP suka tsaya da su lokacin da suke cikin bukata, rahoton Daily Trust.

A hira da manema labarai bayan komawar Matawalle APC, yace:

"Zan cigaba da kasancewa da jam'iyyarmu da kuma mutanen da suka tsaya tare da mu lokacin da muke cikin bukata.
Zam jure dukkan abinda ya fado min sakamakon wannan shawara da na yanke

DUBA NAN: PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

Mataimakin gwamnan Zamfara
Da duminsa: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara Hoto: @Gusau
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari, ya yi tsokaci kan komawar Matawalle APC

Ya ce ya yanke cigaba da zama a PDP ne bayan tattaunawa mai zurfi da abokansa, iyalansa da jam'iyyar.

Gusau yace Matawalle bai nemi shawararsa ba kuma shi kansa jita-jita kawai yake ji.

Ya ce da gayya aka ki sanar da shi kuma wani shiri ne na haddasa kiyayya tsakaninsu, a wata riwayar.

Matawalle ya bi ta kan Yari, ya zama jagoran APC a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

A wani taron gangami da aka shirya wa gwamnan na Zamfara a Gusau, babban birnin jihar, a ranar Talata, Mai Mala Buni, gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin riko na APC ya gabatar da tutar APC ga Matawalle.

Buni ya alanta Matawalle a matsayin sabon jagoran APC a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel