Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari, ya yi tsokaci kan komawar Matawalle APC

Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari, ya yi tsokaci kan komawar Matawalle APC

  • Daga karshe, tsohon gwamna Yari ya amince da shigowar Matawalle APC
  • A bayan Yari yace idan Matawalle ya shiga APC zai rasa kujerarsa
  • Kotun Koli tayi watsi da nasarar APC a zaben 2019 kuma hakan ya ba Matawalle daman hawa kujeran

Tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari, a ranar Litinin ya yi maraba da magajinsa, gwamna Bello Matawalle, zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Ana sa ran Matawalle zai sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Talata.

Yari, a ganawar da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar shiyar Zamfara suka yi a Kaduna, ya ce suna lale marhabun da Matawalle zuwa APC, rahoton Premium Times.

Bayan zaman masu ruwa da tsakin, ya bayyanawa manema labarai cewa mambobin APC sun shirya amsan gwamnan da mabiyansa.

DUBA NAN: Jerin Sabbin Alkalan kotun daukaka kara da CJN Tanko ya rantsar ranar Litinin

Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari
Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari, ya yi tsokaci kan komawar Matawalle APC Hoto: Premium Times
Asali: UGC

DUBA NAN: Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

Yace:

"Wannan zai karawa jam'iyyar mabiya nan gobe. Muna kyautata zaton cewa zuwansa zai amfanar da jam'iyyar a jihar. Saboda hakan muna masa maraba."
"Ba zamu yanke shawara kan komai ba tare da amincewar al'ummarmu ba, shiyasa muka gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki. Ba zamu yarda da komai ba sai dai idan zai amfani jam'iyyar da jihar."

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai tsohon gwamnan jihar, Alhaji Mamouda Shinkafi.

Shinkafi yace shigowar Matawalle jam'iyyar alkhairi ne ga al'ummar jihar, riwayar Daily Trust.

PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC

Gabanin shirin sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP, zuwa APC, babbar jam'iyyar adawar (PDP) ta gargadi gwamnan kan wannan matakin, tare da barazanar yin mai yiwuwa don kare dokokin jam'iyya.

PDP ta gargadi Bello Matawalle da ya sani cewa take-takensa sun yi daidai da shawarar barinsa kujerar mulki saboda an zabe shi a karkashin jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel