Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

  • Babbar jam'iyyar adawa, PDP ta rasa daya daga cikin manyan mambobinta daga jihar Zamfara a majalisar dokokin tarayya
  • Hassan Mohammad Nasiha, mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, ya mika takardar murabus din sa a matsayin dan jam’iyyar PDP
  • Nasiha a cikin wasikar ya bayyana cewa shawarar tasa ta zama dole saboda rugujewar dimokiradiyyar cikin gida ta jam'iyyar

Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta Tsakiya a majalisar dokoki ta kasa, Sanata Hassan Mohammed Nasiha, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Dan majalisar ya sanar da sauya shekarsa a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, 29 ga watan Yuni, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar rasit ta nuna ‘yan siyasa na biyan kudi kafin su zama mambobin jam’iyya a baya

Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar
Sanata Mohammed Hassan Nasiha ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP Hoto: Arise News
Asali: UGC

Ya ce ya shawararsa ta ficewa daga PDP ya zama dole saboda rugujewar dimokiradiyyar cikin gida da rabuwar kan PDP a jihar ta Zamfara.

Sanata Muhammed, a cikin wasikar, bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba.

Yana daga cikin ‘yan majalisar daga jihar Zamfara da ake sa ran za su bi gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Guguwar sauyin sheka: APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3, jam’iyyar adawa ta yi martani

Jagoran APC a Zamfara, AbdulAziz Yari, ya yi tsokaci kan komawar Matawalle APC

A wani labarin, tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari, a ranar Litinin ya yi maraba da magajinsa, gwamna Bello Matawalle, zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Ana sa ran Matawalle zai sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Talata.

Yari, a ganawar da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar shiyar Zamfara suka yi a Kaduna, ya ce suna lale marhabun da Matawalle zuwa APC, rahoton Premium Times.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng