Buhari ya yi martani kan barazanar da Niger Delta Avengers ta yi na gurgunta tattalin arzikin Nigeria
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci tsagerun Neja Delta su mayar da takubansu su dena yi wa kasa barazana
- Shugaban kasar ya ce babu bukatar sabbin barazana a yanzu duba da cewa ya amince ya biya musu kusan dukkan bukatunsu
- Shugaba Buhari, a ranar Juma'a 25 ga watan Yuni ya gana da shugabannin Neja Delta a fadarsa a Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana barazanar da kugiyar Niger Delta Avengers ta yi na fara kaiwa rijiyoyin man fetur da wasu kayyayakin hari a yankin kudu maso kudu a matsayin abin da 'ba a bukatarsa' a yanzu, The Cable ta ruwaito.
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, a shafinsa na Facebook ya ce shugaban kasar ya tattauna da shugabanin kungiyar yan Niger Delta da Ijaw, INC, a fadarsa a ranar Juma'a.
DUBA WANNAN: An kama ƙasurgumin dillalin da ke sayarwa 'yan bindiga makamai a Katsina
Sun ce yankin na kudu maso kudu shine mafi koma baya wurin cigaba a kasar kuma ba a yin wani yunkurin samar da bukatunsu.
A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Asabar, ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka mata.
Ta kuma nuna kin amincewarta da kungiyar Pan Niger Delta Forum, PANDEF, da Cif Edwin Clark ke yi wa jagoranci.
Buhari, ta bakin kakakinsa Femi Adesina, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce ya riga ya dauki mataki a kan mafi yawancin batutuwan da yan bindigan na Neja Delta suke kokawa a kai.
KU KARANTA: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika
Sanarwar ta Buhari ta ce abin daure kai ne ganin sabbin barazana daga kungiyar kasa da awanni 48 bayan ganawarsa da shugabanin yankin Neja Delta inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin kamar sauya tsarin mulki da zaben kwamitin NDDC.
Buhari ya yi wa tawagar na yankin Neja Delta alkawairn cewa gwamnatinsa na aiki tukuru don ganin an biya musu bukatunsu da suka shafi matsalolin muhalli, cigaba da yankin da sauransu.
Ya kuma nemi hadin kai da goyon baya daga shugabannin yankin da mutane domin ganin ba a sake bannatar da kudade ba a hukumar kamar yadda aka yi a baya.
Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari
A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.
A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.
An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.
Asali: Legit.ng