'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

  • Mutanen Olopa Estate a jihar Osun sun tsinci wata wasika da ke cewa yan fashi za su kawo musu ziyara
  • Wasikar wadda aka rubuta da yarbanci da turanci ta ce su tara N20m su bawa mai unguwa ya ajiye wa barayin idan ba su son a ziyarci gidan kowa
  • Hukumar tsaro ta Amotekun ta ce ta samu labarin wasikar amma tana ganin cika baki ne duk da haka ta tsaurara matakan tsaro

Mutanen unguwar Olopa Estate da ke Ofatedo a karamar hukumar Egbedore a jijar Osun suna zaman dar-dar bayan samun wata wasika da ke cewa yan fashi za su zo unguwar sata, Vanguard ta ruwaito.

A cikin wasikar wanda aka rubuta wani sashinsa da harshen yarabanci, an umurci mutanen unguwar su tara Naira miliyan 20 su bawa mai unguwa ya ajiye wa yan fashin idan ba su son a bi su gida-gida.

Taswirar jihar Osun
Taswirar jihar Osun. Hoto: Vangaurd
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan babban bankin Nigeria ya lallasa abokan hammayarsa ya zama dan takarar gwamnan APGA

Wasikar ta ce:

"Sanarwa, muna son sanar da ku cewa mu barayi muna nan zuwa mu yi fashi a kowanne gida a unguwarku ko kuma ku tara Naira miliyan 20 ku bawa mai unguwa mu tafi wurinsa mu karba idan mun zo.
"Za mu zo da karfinmu kuma za mu kashe dukkan masu tsaronku idan suka ce za su dame mu."

Abinda mazauna unguwar suka ce game da wasikar

Wani mazaunin unguwar, Tejumade Adewale ya ce wasikar ya janyo rudani sosai a unguwar har ta kai ga wasu sun dena kwanciya a gidajensu.

"Duk da haka, an karo yan banga, wasu mutanen su kan zo ne kawai da rana su dauki wani abu su koma shagonsu su kwana.
"Muna kira ga jami'an tsaro su zo su taimaka mana kuma kada a yi wasa da barazanar," in ji shi.

KU KARANTA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Matakin da Amotekun ta dauka

Sahara Reporters ta ruwaito cewa Kwamandan Amoketun na Osun, Kwamared Amitolu Shittu ya ce hukumar ta san da batun wasikar kuma ta shirya wa 'bakin'.

Ya kara da cewa barazanar ba wani abu bane amma duk da haka an tanadi jami'an tsaro don dakile harin.

"Mun ji barazanar, muna ganin cika baki ne kawai, duk da haka, an tsaurara matakan tsaro a unguwar don gudun bacin rana," in ji shi.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164