An kama ƙasurgumin dillalin da ke sayarwa 'yan bindiga makamai a Katsina

An kama ƙasurgumin dillalin da ke sayarwa 'yan bindiga makamai a Katsina

  • Rundunar yan sandan Jihar Katsina tayi nasar damke masu safarar bindigu ga manyan yan bindiga a sassan kasar nan
  • Shugaban tawagar masu safarar, wani Ibrahim Abdullahi mai shekaru 40 ya ce suna karbar N100,000 akan kowace bindiga daya
  • An kama kudi kimanin Naira miliyan uku tare bindiga kirar AK47 a tare da su da wasu makaman

Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta cafke wani mutum mai shekara 40, Ibrahim Abdullahi tare da wasu mutane uku da ake zargi da safarar bindigu ga yan bindiga a sassa daban-daban na kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gambo Isah, yayin da yake gabatar da wanda ake zargin ranar Juma'a, yace sun samu kudi kimanin N3,445,000 da kuma bindiga kirar AK47 a wajen wanda ake zargin, rahoton Tribune.

Yan sandan Nigeria
Yan sandan Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

Isah ya bayyana cewa yayin ake tuhumar su, shugaban tawagar, Ibrahim Abdullahi, ya amsa laifin, tare da bayyana cewa shi da tawagar tasa sun kai bindigu shida kirar AK47 ga wani shaharren dan bindiga, Tukur Rabiu, wanda ke boye a dajin Rijana, titin Kaduna zuwa Abuja kuma kudin da aka kama na wadannan kayak ki ne.

Ya ce:

"Wanda ake zargin kuma ya shaida cewa suna kai wa wani Abu Rade, mashahurin dan bindiga da ke boye a dajin Rugu/Dumburum a jihon Katsina da Zamfara.
"Ya kuma kara da cewa yana karbar N100,000 a matsayin kudin kowacce bindiga da yayi safara
"Ya kuma tabbar da cewa suna kai bindiga sansanonin yan bindiga a sassa da dama fadin kasar nan.

KU KARANTA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Isa ya kuma bayyana cewa sun kama AK47, shanu 12 da tumaki 11, a wani yunkurin garkuwa da dabbobi yayin da yan gun-gun yan bindiga, akan babura, suka kai hari kauyen Tinya, karamar hukumar Batsari a jihar Katsina tare da satar wasu dabbobi.

"Wata rundunar hadin gwiwa ta yan sanda da jami'an vigilante sun kora yan bindiga, tare da musayar wuta, wanda yayi sanadiyar mutuwar dan bindiga daya" a cewar sa.

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: