Bana Son Sake Jin Yan Bindigan da Ba'a San Su Ba, Gwamna Ya Gargadi Yan Sanda
- Gwamnan jihar Plateau, Lalong ya samar da sabbin motoci da babura ga jami"an yan sanda
- Lalong ya shaida wa yan sandan baya son ya sake jin ance ba'a san yan bindiga ba
- IGP Usman Baba, yace jami'ansa zasu yi amfani da wadannan kayan aiki ta inda ya dace
Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau, ya fada wa yan sanda cewa baya son ya sake jin "Yan bindigan da ba'a san su ba" nan gaba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhar ya JAddada
Akwai babban kalubalen tsaro a kasa, kuma mafi yawancin lokaci wadanda ke aikin kai hari ana kiran su da 'yan bindigan da ba'a san su ba'
Gwamnan yayi wannan magana ne a yayin jawabinsa wajen taron mika kayan aiki da gwamnatinsa ta samar wa yan sanda a gidan gwamnati dake Jos.
Lalong yace gwamnatinsa ta yi wannan kokarin ne domin ta kara wa hukumomim tsaron jihar kwarin guiwa musamman wajen dakile harin yan ta'adda.
Yace: "Mun fahinci cewa yayin da muke kokarin tabbatar da zaman lafiya, su kuma yan ta'adda basa bacci saboda matakan da muke dauka yana karya kasuwancin su. saboda basa hutawa suna ta kokarin nemo wata hanyar."
IGP yayi alakwarin kare rayuwaka da dukiyoyin mutanen Plateau
Yayin da sufetan yan sanda na kasa, Usman Baba, ya kai ziyara jihar Plateau ranar Litinin, ya tabbatar wa mutanen jihar cewa hukumarsa zata kara kaimi wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu.
KARANTA ANAN: Gwamna Ya Tona Asirin Yan Bindiga, Ya Bayyana Inda Suka Fito da Manufar Zuwan Su Najeriya
IGP ya bada wannan tabbacin ne yayin kaddamar da motocin sintiri 50 da mashina 200 da gwamnan jihar ya samar wa yan sanda domin inganta tsaro a jihar.
Yace: "Ka kalubalance mu daka samar mana da wadannan muhimman kayan aikin, amma inason in tabbatar maka mai girma gwamna samar da wadannan kayan aikin ba zai tafi a banza ba."
"Bada jimawa ba zamu kara daukar sabbin yan sanda, sannan zamu baiwa bangaren bada horo na hukumar mu muhimmanci sosai."
A wani labarin kuma Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓutar da Malami da Wasu Dalibai
Sojoji sun sake fafatawa da ɓarayin ɗaliban FGC Birnin Yauri, sun kuɓutar da malami da ɗalibai uku, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Kakakin rundunar sojin ƙasa, Nwachukwu, yace an sake tura ƙarin sojoji yankin domin hana maharan tserewa.
Asali: Legit.ng