Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci
  • Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su
  • Buhari ya ƙara da cewa gwamnatinsa na iyakacin kokarinta wajen inganta rayuwar yan Najeriya da magance ƙalubalen tsaro

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace dukkan waɗannan bara gurbin dake ɗaukar makami su yaƙi Najeriya zasu fuskanci hukunci, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya

Da yake jawabi a wurin taron matasan APC wanda ya gudana cibiyar taron ƙasa da ƙasa dake Abuja ranar Litinin, Buhari yace gwamnatinsa na iya ƙoƙarinta wajen magance ƙalubalen tsaro da ya addabi ƙasar nan.

Shugaba Buhari
Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari Hoto: @bashirahmad
Asali: Instagram

Shugaba Buhari, wanda sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya wakilta, yayi kira ga matasan su yi aiki tuƙuru domin gyara goben su da kuma ƙasar su.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Tona Asirin Yan Bindiga, Ya Bayyana Inda Suka Fito da Manufar Zuwan Su Najeriya

Yace: "Kamar yadda na faɗa kwanan nan, duk wani ɗan ta'adda dake ɗaukar makami ya yaƙi Najeriya, zai fuskanci hukunci dai-dai da abinda ya aikata."

Buhari ya nuna jin daɗinsa da ayyukan matasan APC

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yayi matuƙar farin ciki da har matasan APC suka yi tunanin shirya irin wannan taron.

Yace: "Ku cigaba da nuna juriya domin gina ƙasar mu, ku tuna bamu da wata ƙasa da ta fi Najeriya. Ya rataya a wuyan kowa mu yi aiki iyakar iyawar mu domin kawiocigaba mai amfani ga ƙasar mu."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

Yan bindigan da suka yi awon gaba da ɗalibai a FGC Birnin Yauri sun saki hotunan waɗanda suka kama, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A makon da ya gabata ne maharan suka dira makarantar sakandiren, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel