Yanzu-Yanzu: DSS ta saki mawaƙin Kano da ya 'zagi' Annabi

Yanzu-Yanzu: DSS ta saki mawaƙin Kano da ya 'zagi' Annabi

  • Hukumar yan sandan farar hula, DSS, ta saki mawaki Ahmad Abdul da ta kama kan zargin batanci
  • Ismaila Na'aAbba Afakallah, shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano ya tabbatar da sakin mawakin
  • Afakallah ya ce ba a gurfanar da mawakin a gaban kuliya ba saboda ya riga ya nemi afuwa, ya tuba ya kuma yi alkawarin ba zai sake ba

Hukumar yan sandan farar hula, DSS, ta sako mawakin addinin musulunci, Ahmad Abdul, da aka kama saboda fitar da wani waka mai dauke da batanci ga Annabi Muhammad (SAW), Daily Trust ta ruwaito.

An kama Abdul ne bayan fitar da wani waka mai taken 'Barhama Gwaska' da ake yi wa kallon ya yi batanci ciki kuma wakar na iya tada rikici a jihar.

Yanzu-Yanzu: DSS ta saki mawakin Kano da ya 'zagi' Annabi
Yanzu-Yanzu: DSS ta saki mawakin Kano da ya 'zagi' Annabi
Asali: Original

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

Da ya ke tabbatar da sakin a ranar Litinin, Sakataren hukumar tantance fina-finai da bidiyo na jihar Kano, Ismaila Na'aAbba Afakallah ya ce ya samu korafe-korafe da dama game da wakar daga mutane.

Daily Trust ta ruwaito cewa Afakallah ya ce ya sanar da DSS game da korafin hakan yasa suka kama mawakin a wani otel da ya boye domin tsoron kada mutanen gari su kai masa hari.

Ya kara da cewa an sada mawakin da yan uwansa bayan shafe kwanaki a hannun DSS.

"An sake shi, ya ce ya yi nadamar fitar da wakar kuma ya nemi afuwa, ya yi alkawarin ba zai sake maimaitawa ba," in ji Afakallah.

Dalilin da yasa ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba

A kan dalilin da yasa hukumar ta ce bata gurfanar da shi a kotu ba, Afakallah ya ce, "Ba gurfanar da mutane a kotu bane ke gaban mu, burin mu shine su tuba su gyara halayensu. Ya yi nadamar abin da ya yi kuma ya nemi afuwa game da laifin da ya aikata."

KU KARANTA: Da Duminsa: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Wannan dai ba shine karo na farko da aka kama mutane kan yin wakar da ake yi wa kallon batanci ga Annabi ba.

A Augustan bara, babban kotun shari'a da ke Hausawa Filin Hockey a jihar Kano ta yanke wa wani Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa bayan samunsa da laifin fitar da wakar batanci a dandalin WhatsApp.

A wani rahoton, mutane da dama da kungiyoyi sun yi Allah wadai da kutsen da aka yi a babban kotu da ke Warri, da ake zargin ƴan ƙabilar Itsekiri magoya bayan Olu na Warri da aka zaɓa, Yarima Tsola Emiko ne suka yi a ranar Alhamis.

The Nation ta ruwaito cewa lauya mai kare hakkin bil adama, Mr Oghenejabor Ikimi ya yi tir da kutsen da ya kira gidadanci da rashin girmama kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel