Da Duminsa: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Da Duminsa: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

  • Masu zanga-zangan neman Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus wato 'Buhari Must Go' sun sake yin zanga-zanga a Abuja
  • A wannan karon sun yi zanga-zangan ne a safiyar ranar Litinin inda suka cinna wuta a titin Musa Yar'Adua Way da ake bi zuwa filin tashin jiragen sama
  • Masu zanga-zangar na rike da takardu da ke dauke da kokensu da kuma dalilan da yasa suke son shugaban kasar ya yi murabus

Wasu masu zanga-zanga a Umaru Yar'Adua Way, babban birnin tarayya Abuja, a safiyar ranar Litinin sun banka wuta a kan titi, hakan ya janyo cinkoson ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito.

Titin na Musa Yar'Adua Way ne ake bi idan za a tafi filin tashi da saukan jiragen sama a birnin tarayyar Abuja.

Masu Zanga-Zagar 'Buhari Must Go' a Abuja
Masu Zanga-Zagar 'Buhari Must Go' a Abuja Sun Cinna Wuta a Titi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

The Cable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar suna ta ihu cewa 'Buhari Must Go' ma'ana 'Dole Buhari Ya Tafi' yayin da suke dauke da takardu masu rubutu daban-daban na nuna rashin kaunar kasancewar shugaban kasar a kan mulki.

Masu motoci da sauran ababen hawa sun rika yin dabaru suna kaucewa wutar da aka kunna a tsakiyar titin.

A shekarar bara an taba yin zanga-zanga makamancin wannan a ranar June 12 inda aka kama da yawa cikin masu zanga-zangar.

Omoyele Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mai jagorancin yan zanga-zangar #RevolutionNow, daga bisani ya wallafa hotuna da bidiyon masu zanga-zangar a shafukansa na sada zumunta.

KU KARANTA: Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

Abin da masu zanga-zangan ke bukata

Masu zanga-zangar suna neman gwamnati ta kawo karshen kallubalen rashin tsaro, mulki mara kyau, saba doka ba tare da hukunci ba, janye dakatarwar da gwamnati ta yi wa shafi Twitter da wasu matsaloli da suka lissafa a takardun da suke dauke da su.

Zanga-zangar na Buhari Must Go ya ja hankulan mutane da dama a yankunan kasar tare da neman Shugaban kasa ya yi murabus musamman a lokacin da hare-haren yan bindiga da satar mutane don kudin fansa ke yawaita.

A wani labarin daban, kun ji cewa daya daga cikin daliban da yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

The Cable ta ruwaito cewa Abubakar Abdulkadir, mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa a arewa maso yamma ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Juma'a.

Kawo yanzu ba a tantance adadin daliban da yan bindigan suka sace ba yayin harin da suka kai a ranar Alhamis. Sai dai, wasu kafafen watsa labarai a Nigeria sun bayyana cewa dalibai 30 ne aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164