'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

  • Yan bindiga sun halaka dagacin kauyen Dogon Daji da ke karamar hukumar Sanga na jihar Kaduna
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da rasuwar basaraken tare da mika sakon ta'aziyya ga al'ummar garin
  • Kwamishinan tsaro da harkokin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce hukumomin tsaro sun fara bincike kan kisar

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Anja Mallam, Dagacin kauyen Dogon Daji a karamar hukmar Sanga a jihar Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun kashe basaraken ne yayin wani harin da suka kai gidansa a ranar Lahadi 20 ga watan Yuni.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar Jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

Martanin gwamnatin Kaduna game da kisar

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa ta samu rahoto daga hukumomin tsaro.

A cikin sanarwar da ta fitar, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya ce yan bindigan sun kutsa kauyen ne suka tafi gidan dagacin kauyen suka bude masa wuta a lokacin da suke kusa da shi hakan ya yi sanadin rasuwarsa.

KU KARANTA: 'Yan daba sun kutsa cikin kotu sun fatattaki alƙali saboda rikicin sarauta

Aruwan ya ce:

"Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi bakin cikin samun labarin, ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan ran mamacin. Gwamnan ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da daukakin jama'an Dogon Daji bisa mummunan kisar da aka yi wa dagacin."

Kwamishinan ya kara da cewa tuni jami'an tsaro sun fara bincike a kan lamarin.

A wani labarin daban, kun ji cewa daya daga cikin daliban da yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

The Cable ta ruwaito cewa Abubakar Abdulkadir, mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa a arewa maso yamma ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Juma'a.

Kawo yanzu ba a tantance adadin daliban da yan bindigan suka sace ba yayin harin da suka kai a ranar Alhamis. Sai dai, wasu kafafen watsa labarai a Nigeria sun bayyana cewa dalibai 30 ne aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164