Jami'an SSS Sun Sake Cafke Wani Mawaki da Ya Zagi Annabi a Jihar Kano

Jami'an SSS Sun Sake Cafke Wani Mawaki da Ya Zagi Annabi a Jihar Kano

  • Hukumar SSS ta cafke wani mawaki da ya rera wata wakar da ta soki mutuncin Annabi
  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, ta karbi korafe-korafe kan wakar mara dadin ji
  • SSS ta ce mawakin ya nuna nadama ya kuma nemi gafarar al'ummar musulmi baki daya

Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ta sake cafke wani mawaki mai suna Ahmad Abdul, a kan wata waka da ake jin ta soki Annabi kuma za ta iya haifar da rudani a jihar Kano.

Jami'an SSS din sun ce sun dauki Abdul ne a hannun jami'an tsaro don kauce wa mummunan abinda zai faru dashi daga mazauna Kano, Premium Times ta ruwaito.

Yayin da yake tsare, Abdul ya nemi gafarar daukacin al'ummar musulmi, gwamnatin jihar Kano da malaman addinin Islama.

Ya gaya wa SSS cewa bai gane cewa wakar ta saba wa koyarwar Musulunci ba.

KU KARANTA: Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan bindiga sun kashe da dama a jihar Neja

An Kuma: SSS Sun Cafke Wani Mawaki da Ya Zagi Annabi a Jihar Kano
Jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake tsokaci, Sakataren zartarwa na Hukumar Tantancewa ta Jihar Kano, Ismaila Afakallah, ya ce ya karbi daruruwan korafe-korafe a kan wakar daga ‘yan jihar.

Afakallah ya ce ya kai karar mawakin ga jami’an SSS wadanda suka cafke shi a wani otal da ya boye tsawon kwanaki.

Mahaifin mawakin, Abdullahi Isa, ya gode wa hukumar ta SSS saboda dauke matakin da ta yi a kan lokaci wanda ya kauce wa barkewar doka da oda.

A watan Agustan da ta gabata, wata babbar kotun shari’ar Musulunci da ke yankin Hausawa Filin Hockey a jihar ta samu wani mawaki, Yahaya Sharif-Aminu da laifin sukar Annabi kuma ta yanke masa hukuncin kisa saboda wata waka da ya yi, kamar yadda yazo a rahoton BBC.

Sai dai, bangaren daukaka kara na Babbar Kotun Jihar Kano a ranar 21 ga Janairu sun yi watsi da hukuncin kisan tare da sakin mawakin.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kira iyayen daliban kwalejin Kebbi, sai dai basu nemi fansa ba

Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya

A wani labarin, Kasar Birtaniya tayi Allah-wadai da hukuncin kisan da kotun Shari'a ta yankewa mawakin nan dan jihar Kano, Yahaya Sharif-Aminu.

Kasar ta Birtaniya ta ce mawakin yana da 'yancin da zai iya nuna ra'ayinsa sannan kuma ya kalubalanci hukumomi, inda ta ce wannan ba komai bane a kasashen da aka cigaba.

A ranar Litinin ne dai kotun Shari'ar ta yankewa Sharif-Aminu mai shekaru 22 hukuncin kisa, bisa laifin zagin Annabi Muhammad (SAW), a cikin wata waka da yayi ya yada a manhajar WhatsApp.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel