Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan bindiga sun kashe da dama a jihar Neja

Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan bindiga sun kashe da dama a jihar Neja

  • Sojojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a wani yankin jihar Neja, sun hallaka da dama
  • An ruwaito cewa, akalla 'yan bindiga 15 ne suka mutu yayin harin, sai dai soja daya shima ya mutu
  • Kai dauki da sojojin suka kawo ya ceto mazauna yankin daga mummunan harinn 'yan bindiga

Akalla 'yan bindiga 15 ne aka hallaka a yayin wata musayar wuta da sojoji a ranar Asabar a Anguwan Mallam da ke Kontagora ta jihar Neja.

Hakzalika, wani jami’in soja ma an kashe shi a yayin artabun, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi daga yankin sun ruwaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin karfe 4 na yamma lokacin da sojoji da ke sintiri a Anguwan Mallam suka ga 'yan ta'addan.

KU KARANTA: Firaministan India Ya Aikewa Buhari wasikar shawari kan lafiyar motsa jiki

Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan bindiga sun kashe da dama a jihar Neja
Sojojin Najeriya a fagen daga | Hoto: tvcnews.tv
Asali: UGC

Majiyoyin sun kara da cewa 'yan ta'addan da yawansu ya haura 70 sun mamaye yankin, amma zuwan sojoji waje ya ceci al'ummomin daga kai musu hari a yammacin Asabar.

Majiyar ta ce:

“Zuwan sojoji shine ya ceci al’ummarmu daga 'yan bindiga. Sun zo da adadi mai yawa a kan babura kuma mutane sun firgita saboda ba mu da abin da za mu iya fuskantarsu.”
“Amma an kashe da yawa, mun gano gawarwaki ko yau da safe a cikin daji. Mun gano kayan bacci da wasu kayayyaki masu daraji."

An ce 'yan bindigan sun tsere cikin daji yayin da sojoji suka fi karfin su. Sai dai, har yanzu ‘yan sanda ba su mayar da martani kan lamarin ba.

Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno

Jirgin yaƙin rundunar sojin sama (NAF), ya hallaka yan ta'addan Boko Haram-ISWAP, cikinsu harda kwamandojin su a Lamboa, ƙaramar hukumar Kaga, jihar Borno, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa jiragen yaƙin NAF masu saukar angulu biyu ne suka yi ruwan bama-bamai kan yan ta'addan, kuma ana tsammanin an kashe sanannen kwamandan ISWAP, Modu Sullum.

An gano cewa gomman mayaƙan ISWAP sun hallaka a yayin harin jiragen yaƙin sojojin sama NAF.

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya tabbatar da nasarar da jiragen yaƙin suka samu.

KU KARANTA: Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

'Yan bindiga sun kira iyayen daliban kwalejin Kebbi, sai dai basu nemi fansa ba

A wani labarin, Rahoto daga jaridar Cable ya bayyana cewa, Isah Arzika, shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Kebbi (NUT), ya ce wadanda suka sace daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, sun tuntubi iyayen yaran.

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun far wa makarantar a ranar Alhamis, kuma suka yi awon gaba da daliban da ba a san yawansu ba bayan arangama da jami'an 'yan sanda dake bakin makarantar, The Gaurdian ta ruwaito.

A baya-bayan na, an kubutar da dalibai biyar da malamai biyu, yayin da dalibi ya mutu a yayin aikin ceto da jami'an tsaro suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.