Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya

Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya

- Kasar Birtaniya ta ce za ta cigaba da sanya ido kwarai da gaske akan hukuncin kisan da aka yankewa mawakin nan dan jihar Kano

- Gwamnatin ta ce bata goyon bayan hukuncin kisa akan kowanne irin laifi da mutum zai aikata

- Ta kara da cewa kowanne mutum yana da 'yancin fitowa ya nuna ra'ayinsa sannan kuma ya kalubalanci hukumomi a wuraren da aka cigaba

Kasar Birtaniya tayi Allah-wadai da hukuncin kisan da kotun Shari'a ta yankewa mawakin nan dan jihar Kano, Yahaya Sharif-Aminu.

Kasar ta Birtaniya ta ce mawakin yana da 'yancin da zai iya nuna ra'ayinsa sannan kuma ya kalubalanci hukumomi, inda ta ce wannan ba komai bane a kasashen da aka cigaba.

Muna sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda y zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya
Muna sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda y zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya
Asali: Facebook

A ranar Litinin ne dai kotun Shari'ar ta yankewa Sharif-Aminu mai shekaru 22 hukuncin kisa, bisa laifin zagin Annabi Muhammad (SAW), a cikin wata waka da yayi ya yada a manhajar WhatsApp.

Wannan hukunci da kotun ta yanke ya jawo kace-nace matuka a Najeriya, inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama suka dinga Allah wadai da wannan hukunci.

Kotun Shari'ar dai ta bukaci gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje akan ya sanya hannu akan hukuncin kisan da ta yanke.

Da take tofa albarkacin bakinta akan hukuncin kisan da aka yanke bayan wata tambaya da wakilin jaridar PUNCH yayi a ranar Laraba, ofishin jakadancin kasar Birtaniya dake Najeriya ya ce zai cigaba da sanya ido akan wannan lamari.

KU KARANTA: Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati

A wani sako na yanar gizo da jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin kasar ta Birtaniya, Christopher Ogunmodede, ya aika, ya ce gwamnatin kasar Birtaniya bata goyon bayan hukuncin kisa akan kowanne irin laifi.

Sakon ya ce: "Kasar Birtaniya tana kokari wajen kare hakkin imani akan addini a ko ina a fadin duniya, kuma tana fitowa tayi magana a duk inda taga ba daidai ba domin kare wannan hakki.

"Mun yadda cewa kowanne mutum yana da 'yancin da zai iya fitowa ya nuna ra'ayinsa, sannan kuma ya kalubalanci hukumomi a duka wuraren da aka samu cigaba. Zamu cigaba da sanya ido akan lamarin sosai. Tsari ne da ya jima a kasar Birtaniya wajen ganin ta kare hakkin dan adam ta kuma hana yankewa kowanne mutum hukuncin kisa akan kowanne irin laifi da ya aikata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel