Yanzu Yanzu: Neman ballewa: Gwamnonin kudu maso gabas sun yi Allah wadai da IPOB, suna son hadaddiyar Najeriya

Yanzu Yanzu: Neman ballewa: Gwamnonin kudu maso gabas sun yi Allah wadai da IPOB, suna son hadaddiyar Najeriya

  • Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas janye kanta daga kungiyoyin da ke neman ballewa a yankinsu
  • Hakazalika gwamnonin sun yi Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan kiraye-kirayen wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi
  • Sun bukaci Najeriya ta ci gaba a matsayin tsintsiya madaurinta daya

Membobin Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas sun nesanta kansu daga kungiyoyin da ke kira ga ballewa a yankin da sauran sassan kasar.

Sun kuma yi Allah wadai da rikice-rikicen da suka biyo bayan tashin hankalin wanda ya kai ga asarar rayuka da asarar dukiyoyi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar ASUU na barazanar shiga sabon yajin aiki, sun bayyana dalili

Yanzu Yanzu: Neman ballewa: Gwamnonin kudu maso gabas sun yi Allah wadai da IPOB, suna son hadaddiyar Najeriya
Gwamnonin kudu maso gabas sun nesanta kansu da kungiyoyin da ke neman a raba kasar Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Gwamnonin sun hadu ne a ranar Asabar, 19 ga watan Yuni, a jihar Enugu domin tattaunawa kan hanyoyin magance matsalolin tsaro da maido da zaman lafiya a yankin.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya yi magana a madadin gwamnonin a karshen taron inda yace:

“Mun yi tir da duka ayyukan kungiyoyin masu neman ballewa a Kudu maso Gabas da sauran wurare.
“Mun tabbatar da cewa ba ma goyon bayansu, ba da yawun Kudu maso Gabas suke magana ba.
“Tunanin cewa shugabannin Kudu maso Gabas sun yi shiru a kan neman ballewar wasu daga cikin matasanmu ba daidai ba ne.
“Gwamnonin Kudu maso Gabas, Shugaban Ohanaeze, mambobin Majalisar Tarayya, mashahuran shugabanni sun fito fili a lokuta da dama a baya don yin magana game da irin wannan hargitsi.
"Don kar a lalata halin da ake ciki mara dadi, shugabannin Kudu maso Gabas sun kafa wani kwamiti da zai tattauna da irin wadannan matasa don su tsaya su bar dattawa su yi magana don magance irin wannan fargaba."

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa sata, cin hanci da rashawa - Kwamitin Majalisar Dattijai

Sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da ayyukansu a bisa ka'idojin aiki da doka.

Sun kuma bukaci mambobin majalisar kasa daga yankin Kudu maso Gabas da su goyi bayan kirkirar ‘yan sanda na jihohi a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ke gudana.

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya gano rashin amana da adalci a matsayin wani bangare na dalilan da ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Yuni, a yayin bude taron tattaunawar masu ruwa da tsaki na kwanaki biyu game da batun samar da zaman lafiya ga jihohin Taraba, Benuwai da Nasarawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A taron da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, Gwamna Sule na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce tun da ya hau mulki, bai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel