Ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa sata, cin hanci da rashawa - Kwamitin Majalisar Dattijai

Ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa sata, cin hanci da rashawa - Kwamitin Majalisar Dattijai

  • Ma’aikatan gwamnati sun fi kowa satar kudaden gwamnati a kasar nan
  • Dan Majalisar Dattijan ya ce ‘yan siyasa ba su kai kashi 10 na al’ummar kasar nan ba
  • Ya ce binciken ya gano biliyoyin naira aka karkatar da akalarsu a ma’aikatu da kafofin gwamnati

Kwamitin kula da kudaden gwamnati na Majalisar Dattijai ya bayyana cewa sakamakon binciken da ya gudanar ya gano cewa ma’aikatan gwamnati sun fi aikata cin hanci da rashawa idan aka kwatanta da ‘yan siyasar kasar nan.

Shugaban kwamitin Sanata Matthew Urhoghide, shi ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da jaridar Punch a Abuja.

Kwamitin wanda shi ne kadai kwamitin Majalisar Dattijai da tsarin mulki ya yi na’am da shi, a halin yanzu yana kan aikin kalailaice rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya na 2015 zuwa 2018.

Rahoton Mai Binciken Kudin Tarayyar ya kunshi binciken da ya gudanar kan asusun ajiyar ma’aikatu da cibiyoyin da kuma kafofin gwamnatin tarayya.

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa cin hanci da rashawa - Kwamitin Majalisar Dattijai
Ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa cin hanci da rashawa - Kwamitin Majalisar Dattijai

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Sanata Urhoghide ya koka cewa sakamakon Binciken Kwamitin ya gano mafi munin cin hanci da rashawa wanda ya yi wa lakabi da suna ‘cin hanci da rashawan cibiyoyi’ yana faruwa ne a bangaren aikin gwamnati.

Ya ce:

“Bari in bayyana wannan abin, muna a lokacin da ake gaggawar yin zarge-zarge, inda mutane suke hanzarin tsinuwa musamman a kan ‘yan siyasa.
“Kowa ya imanin cewa duk wata aika-aika a kasar nan ‘yan siyasa ne ummul haba’isinta, amma za mu ci gaba da fada musu cewa idan ka tattara dukkanin jam’iyyun siyasar kasar nan da daukacin mambobinsu, ba su kai kashi 10 na al’ummar Najeriya ba. Don haka ba mu ba mune da rinjaye a kasar nan ba.
“Abin da kwamitinmu ya gano shi ne sace kudin gwamnatin da ake yi ba ‘yan siyasa ne ke satar su ba.
“Mun gano biliyoyin nairar da aka sace daga cikin asusun ma’aikatu da kafofin gwamnati.
“Dan Allah, ‘yan siyasa nawa ne suke da wadannan makudan kudaden?

Ya ce suna gayyatar jagororin ma’aikatu wadanda su ma’aikatan gwamnati ne domin su yi musu bayanin kudaden da aka sace.

Mun gano biliyoyin naira da aka kashe ba tare da wata kwakkwarar hujjar da doka ta tabadar ba, a cewarsa.

EFCC ta kwato N6bn, Gidaje 30, Motoci 32 a cikin watanni 3

Hukumar yaki da cin hancin tattalin Kasa ta ce kawo yanzu ta gano sama da Naira biliyan 6, da gidaje 30 da motoci 32 tsakanin watan Maris zuwa Yunin bana.

Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin taron karawa juna sani na mako-mako da Kungiyar Tattaunawar Shugaban Kasa ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel