Gwamnan APC ya ambaci abinda ke haddasa rashin tsaro a Najeriya

Gwamnan APC ya ambaci abinda ke haddasa rashin tsaro a Najeriya

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya dauki rashin adalci a matsayin abun da ke haifar da kalubalen tsaro a Najeriya
  • Gwamnan ya bayyana wannan ra'ayi ne a tattaunawar samar da zaman lafiya da aka shirya wa jihohin Taraba, Benuwe da Nasarawa
  • Barista Istifanus Haruna, shugaban ma'aikata na gwamnan jihar Taraba, ya yaba da hadin kan jihohin uku domin hada hannu wajen yaki da matsalar tsaro

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya gano rashin amana da adalci a matsayin wani bangare na dalilan da ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Yuni, a yayin bude taron tattaunawar masu ruwa da tsaki na kwanaki biyu game da batun samar da zaman lafiya ga jihohin Taraba, Benuwai da Nasarawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Na kan yi sallah raka’a 2 a daren Alhamis sai na hada masu yi mana sharri da Allah – El-rufai

Gwamnan APC ya ambaci abinda ke haddasa rashin tsaro a Najeriya
Gwamna Abdullahi Sule yace rashin adalci na daga ikin abunda ke haddasa rashin tsaro a Najeriya Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Asali: Facebook

A taron da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, Gwamna Sule na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce tun da ya hau mulki, bai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.

Ya jaddada bukatar dukkan masu ruwa da tsaki a jihohin uku su hada hannu wajen gina zaman lafiya mai dorewa.

KU KARANTA KUMA: Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa

A jawabinsa, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Taraba, Barista Istifanus Haruna, ya ce zaman lafiya ya kau daga jihohin Taraba, Nasarawa da Benuwe yayin da kowannensu ya fada cikin rikici na lokaci mai tsawo.

Haruna ya yaba da kokarin da gwamnatocin jihohin uku suka yi da nufin hada kai don samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin.

A halin yanzu, Christian Okafor, wakilin shirin Majalisar Dinkin Duniya na Raya Kasa (UNDP), ya ce an shirya taron zaman lafiyar yankin ne tare da kungiyar hadin gwiwar kasashen Afirka ta Yamma don samar da zaman lafiya a Najeriya.

Wadansu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kashe manoma shida a Nasarawa

A wani labarin, kimannin manoma shida aka kashe a wani hari da wadanda ake zargin makiyaya ne suka kai a Karamar Hukumar Keana cikin Jihar Nasarawa.

Da yake tabbatar da kisan, Shugaban kungiyar al’ummar Tibi a Jihar Nasarawa, Kwamred Peter Ahemba ya ce kusan manoma shida ‘yan kabilar Tibi wadansu da ake zargin makiyaya suka kashe.

Ya ce maharan da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan kauyen Tse-Jimin, da ke masarautar Aloshi a Karamar Hukumar Keana da misalin karfe 9:45 na daren jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel