Kungiyar ASUU na barazanar shiga sabon yajin aiki, sun bayyana dalili

Kungiyar ASUU na barazanar shiga sabon yajin aiki, sun bayyana dalili

  • Wata takaddama ta masana'antu tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya na iya faruwa idan har ba a biya bukatun malaman ba
  • Kungiyar ta fitar da sanarwa inda ta bayyana dalilin da zai sa a daura alhakin yajin aikin da suke barazanar zuwa a kan babban akawun tarayya, Ahmed Idris
  • Kwanaki ASUU ta samu rashin fahimtar juna da gwamnatin tarayya game da Hadadden tsarin biyan albashin Ma'aikata

Malaman jami'o'in gwamnati a duk fadin kasar suna barazanar shiga wani sabon yajin aiki.

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi wannan barazanar a lokacin da ta zargi Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da kin biyan albashi da kuma fitar da kudaden alawus na sama da ma’aikata 1000 na tsawon watanni 13, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan APC ya ambaci abinda ke haddasa rashin tsaro a Najeriya

Kungiyar ASUU na barazanar shiga sabon yajin aiki kan rashin biyan albashi
ASUU na barazanar sake shiga yajin aiki saboda rashin biyan albashi Hoto: Federal Ministry Of Labour And Employment
Asali: Facebook

Lazarus Maigoro, shugaban ASUU na jami’ar Jos, ya yi wannan barazanar a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa kungiyar ta zargi babban akanta da rura wutar rikici tsakanin gwamnatin tarayya da malaman.

ASUU ta ce:

"Duk da umarnin da shugaban kasar ya bayar na biyan albashin dukkan malaman jami’ar, AGF ya ki biyan albashinsu da suka fara daga watanni hudu zuwa 13.

KU KARANTA KUMA: Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa

“Babban abin damuwa shi ne yadda yayin da AGF ke kin biyan wadannan albashin, ma’aikatansa a cikin OAGF sun dukufa wajen kiran malaman da abin ya shafa da kuma dagewa kan cewa sai sun yi rajista da IPPIS kafin a biya su; wasu ma ana neman su hakura da wani bangare na albashinsu domin a biya su. Don haka a fili yake cewa wannan wani aiki ne da gangan daga AGF da mukarrabansa.”

ASUU ta yi Allah wadai da korar malaman jami’a da gwamnatin Kaduna ta yi

A wani labarin, kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, ta nuna rashin amincewarta da korar malamai 16 da ma’aikatan jami’ar guda biyu wadanda ba malamai ne ba da gwamnatin jihar ta yi.

An kori ma’aikatan 18 saboda shiga cikin yajin aikin gargadi na kwana biyar da kungiyar kwadagon Najeriya, ta kira a jihar, tsakanin 17 zuwa 19 ga watan Mayu.

Shugaban kungiyar kwadagon a jihar, Peter Adamu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Kaduna ranar Litinin, ya bayyana matakin a matsayin haramtacce, rahoton Daily Nigerian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng