Sardauna ya yi ƙoƙarin haramta wa makiyaya Fulani kiwo a fili, Dr Albasu Kunini

Sardauna ya yi ƙoƙarin haramta wa makiyaya Fulani kiwo a fili, Dr Albasu Kunini

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba Dr Joseph Albasu Kunini ya ce da tuni an dade ta hana kiwo a fili a Nigeria
  • Kunini ya ce Frimiyan farko a Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya yi yunkurin hana kiwon a fili a arewa
  • Dan majalisar ya kuma nuna rashin jin dadinsa ga mutanen da ba su son su amince cewa lokaci ya yi da za a dena kiwo a fili

Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Dr Joseph Albasu Kunini ya yi wani zance da zai bawa mutane da dama a arewa mamaki dangane da batun hana kiwo a fili a arewacin Nigeria.

A cewarsa, tun da dadewa an yi kokarin kawo karshen kiwo a fili a arewa.

Dr Joseph Albasu Kunini
Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Dr Joseph Albasu Kunini. Hoto: Dr Joseph Albasu Kunini
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bana tunanin ƴan Nigeria ne: Ɗaliban makarantar Kebbi ta yi ƙarin haske kan ƴan bindiga

Ya ce, jagoran da ya yi kokarin kawo karshen kiwon a fili ba kowa bane illa Firimiyan Afirka na farko, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Dr Kunini ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na kwana biyu da aka yi don kawo zaman lafiya, a garin Lafia na jihar Nasarawa a cewar rahoton Sun News.

Ya cigaba da cewa batun na kunshe ne cikin wata takarda da aka yi wa lakabi da 'The Industrial Potentials of Northern Nigeria' da Ma'aikatar Kasuwanci da Saka Hannun Jari na Arewacin Nigeria ta rubuta.

Ya ce:

"A lokacin gwamnatin yankin arewa bata goyon bayan kiwo a fili da makiyaya ke yi; misali, a shafi na 155 na takardar mai shafuka 287, gwamnatin yankin arewa karkashin jagorancin Firimiya kuma Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, ta sha alwashin kawo karshen kiwo a fili da makiyaya ke yi."
"A cewar takardar, 'tsawon shekaru gwamnatin arewacin Nigeria ta fara kokarin samarwar makiyaya matsuguni kuma ta fara samun nasara kan hakan."

KU KARANTA: 'Yan daba sun kutsa cikin kotu sun fatattaki alƙali saboda rikicin sarauta

Tsohuwar dokar kiwo a jihohin arewa kawai ta ke aiki - Falana

Lauya mai rajin kare hakkin bil adama, Cif Femi Falana (SAN) ya ce dokar kiwo na shekarar 1964 a jihohin arewa ne kawai ta ke aiki a shekarun 1960s.

Falana ya yi wannan furucin ne kamar yadda Legit.ng ta gani a ranar Litinin 14 ga watan Yuni a yayin da ya ke martani ga shirin shugaba Muhammadu Buhari na farfado da tsohon dokar tare da ginawa makiyaya wuraren kiwo.

Lauyan ya ce dokar ta 'Grazing Reseves Act of 1964' ba a kasa baki daya ta ke aiki ba.

A wani labarin daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya amince da dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na jihar Zamfara (ZAROTA) bayan yawan koke da ake yi da ayyukan jami'an hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

TVC News ta ruwaito cewa daga yanzu rundunar hadin gwiwa ta yan sanda, VIO, FRSC da jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ne za su rika sa ido kan ayyukan ZAROTA, a cewar sakataren dindindin na ayyukan fadar gwamnati, Yakubu Haidara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel