Matawalle ya dakatar da ayyukan hukumar ZAROTA a Zamfara

Matawalle ya dakatar da ayyukan hukumar ZAROTA a Zamfara

  • Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da ayyukan hukumar ZAROTA a zamfara
  • Gwamnan ya dauki wannan matakin ne biyo bayan korafi da zanga-zanga direbobi suka yi kan zargin jami'an hukumar da cin zalinsu
  • Gwamnan ya umurci yan sanda, FRSC, NSCDC da VIO su maye gurbin hukumar ZAROTA kafin a yi bincike kan zargin

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya amince da dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na jihar Zamfara (ZAROTA) bayan yawan koke da ake yi da ayyukan jami'an hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

TVC News ta ruwaito cewa daga yanzu rundunar hadin gwiwa ta yan sanda, VIO, FRSC da jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ne za su rika sa ido kan ayyukan ZAROTA, a cewar sakataren dindindin na ayyukan fadar gwamnati, Yakubu Haidara.

Jami'an ZAROTA a jihar Zamfara
Jami'an ZAROTA a jihar Zamfara suna fareti. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Boko Haram ta naɗa sabon shugaba bayan tabbatar da mutuwar Sheƙau

"Mai girma gwamna ya bada umurnin a kafa kwamiti domin duba yadda jami'an hukumar ke gudanar da ayyukansu."
"Don haka, yana shawartar mutane masu bin doka da oda su cigaba da gudanar da harkokinsu da doka ta halasta," a cewar sanarwar.

Korafe-Korafe kan ayyukan hukumar ZAROTA

Tunda farko, direbobin tanka, a ranar Alhamis, sun rufe hanyar Gusau-Zaria domin yin zanga-zanga a kan abin da suka kira zalunci da jami'an hukumar ke musu a jihar.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga

Matifya da dama ciki har da daliban Jami'ar Tarayya da ke Gusau sun gaza isa wurin da za su tafi saboda rufe hanyar.

Shugabannin direbobin tankan sun ce sun dauki wannan matakin ne bayan sun yi ta shigar da korafi game da abin da jami'an hukumar ke musu amma ba a kula su ba.

Tsohon gwamna Abdulaziz Yari ne ya kafa hukumar domin ta rika tabbatar da dokokin tuki a jihar.

A wani labarin daban kun ji cewa Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya amince da sauke dukkan shugabannin riko na kananan hukumomin a jiharsa daga ranar Juma'a 4 ga watan Yunin shekarar 2021, The Nation ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan karewar karin wa'adin da aka yi musu na watanni shida wadda majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da shi a baya amma yazo karshe a ranar Juma'a.

Ya bukaci shugabannin na kananan hukumomin su mika mulki ga manyan direktoci a hukumominsu ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164