Masu garkuwa sun harbe direba, sun sace mahaifiya da ɗanta a Nasarawa

Masu garkuwa sun harbe direba, sun sace mahaifiya da ɗanta a Nasarawa

  • Wani direban mota, Abdullahi Abubakar, a Nasarawa ya maganta kan yadda masu garkuwa suka tare su a hanya suke bude musu wuta
  • Abdullahi Abubakar ya ce yana tuki kwatsam yan bindigan suka bullo a titin suka bude masa wuta harsahi ta shafi kansa
  • Ya ce harbin da suka masa yasa motar ta kwace masa ya fada daji sannan daga bisani suka zo suka dauke matar da danta

Masu garkuwa da mutane sun harbi wani direba, Abdullahi Abubakar da bindiga sun kuma sace wata mata da danta mai shekaru uku a yammacin ranar Litinin a hanyar Ugya-Umaisha a karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa, Daily Trust ta ruwaito.

Abubakar, yayin da ya ke bada labari a asibiti a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 4.45 na yamma yayin da ya dako matar da danta daga Toto zai kai su Umaisha.

'Yan bindiga
Masu fashin daji. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama hatsabibin ɓarawon da ya yi sata gidaje fiye da 1,000 a Kano

Ya ce masu garkuwa da mutanen da adadinsu ya kai 20 dauke da muggan makamai sun bullo ne a titin suka bude wa motarsa wuta., kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce daya daga cikin harsashin ya gogi kansa nan take motar ta yi kundumbala ta shiga daji.

"Daya daga cikin harsahin da suka harba ya shafe ni a kai sakamakon bude wa mota na wuta da suka yi.

"Nan take motar ta kubce min na fada cikin daji, daga nan suka zo suka dauke matar da danta," in ji shi.

Ya ce yan bindigan sun tafi sun kyalle shi kwance cikin jini bayan sun yi tsamanin ya mutu.

Wani direban, Zakari Musa, wanda ya tsira daga harin masu garkuwar ya sha sun bude wa motarsa wuta sun fasa masa gilashin baya a motarsa kirar Golf mai lamba ST 495 AAA.

KU KARANTA: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

Ya ce ya dako wani soja sanye da kayan farar hula da wasu fasinjoji daga Abaji zuwa Umaisha kawai ya yi kacibus da masu garkuwar, yana mai cewa harsashi ya shafi sojan a wuyansa.

Shugaban sashin watsa labarai na karamar hukumar Toto, Mr Hagai Daniel ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar wayar tarho da wakilin majiyar Legit.ng.

Kakakin yan sandan jihar Nasarawa, ASP Rahman Nansel bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba domin tabbatar da afkuwar lamarin.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel