Kowa ya kare kansa daga 'Yan Bindiga: Matawalle ya faɗawa Zamfarawa

Kowa ya kare kansa daga 'Yan Bindiga: Matawalle ya faɗawa Zamfarawa

  • Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga yan bindiga
  • Matawalle ya ce gwamnatinsa na yin wani shiri inda za a zabi matasa a garuruwa da za su rika kare garin daga mahara
  • Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da masu sarautun gargajiya domin zaben jaruman matasa da za su yi wannan aikin

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara
Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle: Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Ya kara da cewa suna aiki kan tsarin da za a bawa masu rike da sarautun gargajiya damar zaban matasan da za su rika kare garuruwansu daga maharan.

"Ya kamata mutanen gari su rika sa ido su kuma rika tona asirin bata gari da ke cikinsu. Hakan ne zai tabbatar da cewa an gano munafikai da ke zaune cikin mutane.

"Akwai wasu mutanen da ke farin cikin ganin mahara suna kai wa jama'a hari. Idan kana tunanin baka da hannu cikin wannan mummunan aikin toh ka fito da zuciya daya ka rantse da Allah kamar yadda na yi.

KU KARANTA: Da Duminsa: NANS ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi ranar June 12, ta bayyana dalili

"Kare rayyuka da dukiyoyin mutanen jiha na shine abu na farko kuma mafi muhimmanci kuma za mu cigaba da yin hakan da hanyoyin da doka ya halasta don tabbatar da samar da tsaro a wuraren da ake fama da rashin tsaro."

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel