An kama hatsabibin ɓarawon da ya yi sata a gidaje fiye da 1,000 a Kano

An kama hatsabibin ɓarawon da ya yi sata a gidaje fiye da 1,000 a Kano

  • Yan sanda a jihar Kano sun kama wani hatsabibin barawo, Salihu Usman, da ya shafe shekaru yana kutse gidan mutane yana sata
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Kano, Haruna Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin
  • Abdullahi ya ce yan sandan sun kama Salihu Usman ne bayan mutanen garin sun yi korafi a kansa a yanzu yana tsare a hedkwatar yan sanda

Yan sanda a jihar Kano sun kama wani Salihu Usman da ake zargin ya yi sata a gidaje fiye da 1,000 a fadin jihar Kano, The Cable ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Haruna Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.

Taswirar Kano
Taswirar Jihar Kano. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Haruna ya ce wanda ake zargin ya aikata laifukan ne a kimanin shekaru shida kuma ya yi kutse a gidaje da dama a Kurna da wasu unguwanni ya yi sata, rahoton The Cable.

DUBA WANNAN: Da Duminsa: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

"Yadda ya ke sata abin na bawa mutane mamaki. Hasali ma, wasu mutane na cewa yana amfani da asiri ne ko kuma shi fatalwa ne da ke bata kama idan ya zo sata, a cewar kakakin yan sandan.

"Da muka samu korafi kansa daga mazauna unguwa, Samaila Dikko, kwamishinan yan sandan Kano ya bada umurnin a kamo wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba.

"Munyi nasarar kama shi tare da taimakon jami'an tsaro da ke unguwan.

Wanda ake zargin da aka ce shekarunsa 29 ya amsa cewa ya aikata laifukan da ake zarginsa a lokacin da aka yi holensa.

KU KARANTA: Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

"Ina balle gidajen mutane inyi sata amma bana amfani da wani asiri. Na iya buga wasan kwallon kafa sosai, shi yasa na iya gudu sosai," in ji shi.

Yan sandan sun ce an kwato babur, almakashi, karfe, huluna biyu da fitilar torchlight a tare da shi.

Abdullahi ya kara da cewa za a cigaba da ajiye wanda ake zargin a hedkwatan yan sanda da ke Bompai a jihar Kano har sai an kammala bicike sannan a gurfanar da shi.

Kada a biya kudin fansa idan masu garkuwa sun sace ni, Mai dakin El-Rufai

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel