Da Duminsa: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

Da Duminsa: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

  • Yan Boko Haram sun sako Abubakar Garba Idris (Alooma) ma'aikacin Hukumar Kula da' Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR)
  • An kuma sako wasu mutane tara a ranar Litinin 14 ga watan Yuni bayan sun shafe watanni a hannun yan ta'addan
  • Rahoton ya kuma ce babban direktan kungiyoyin taimakawa al'umma na Yobe, Abubakar Baba Shehu ya tabbatar da sako su Alooma

Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta sako babban mataimaki na kariya a Hukumar Kula da' Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Alooma da ta sace a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, The Nation ta ruwaito.

Majiyoyi daga hukumomin tallafawa al'umma sun tabbatar da cewa Alooma yana asibitin dakarun sojoji na Operation Hadin Kai a Maiduguri ana duba shi kafin a sada shi da iyalansa.

Abubakar Garba Idris (Alooma)
Ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya, Abubakar Garba Idris (Alooma). Hoto: The Nation
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sojojin Nigeria na buƙatar addu'a domin yin nasara kan Boko Haram, Janar na Sojoji

Majiyar ta kuma ce an sako dan kasuwa, Mu'azu Bawa, wanda aka sace shi tare da wasu mutane takwas a ranar, duk dai sojoji na musu tambayoyi da duba su.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa babban direktan kungiyar Yobe State Network of Civil Society, Abubakar Baba-Shehu shima ya tabbatar da sako wadanda aka yi garkuwar yana mai cewa 'wannan labari ne mai dadi'.

"Ina tare da wani wanda ya kira dan gidan su Alooma ya kuma tabbatar an sako dan uwansa. Wannan labari ne mai karfafa gwiwa muna fatan za a sako sauran da ake tsare da su nan bada dadewa ba," in ji Shehu.

Idan za a iya tunawa, Legit.ng ta ruwaito yadda maharan suka kaiwa ayarin wasu matafiya hari a kusa da kauyen Matari tsakanin Minok zuwa hanyar Jakana inda aka sace Alooma misalin karfe 8.30 na safiyar Asabar.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan wadanda suka fito sanye da kayan sojoji sun sanya shingen kan hanya a kan babbar hanyar da motocin Hilux guda uku da babura.

Majiyoyin sun ce: “Yayin da ake binciken fasinjojin, Idris ya yi kokarin jefar da katin shaidarsa amma daya daga cikin maharan ya ganshi.

KU KARANTA: Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

"Daga nan aka nemi ya sauka daga motar tare da wasu fasinjoji biyu, yayin da aka nemi sauran fasinjojin da su ci gaba da tafiya.

"Daga baya an saki fasinjojin biyu a kan cewa su talakawa ne sosai kuma ba su da wani amfani da za a sace su."

Kada a biya kudin fansa idan masu garkuwa sun sace ni, Mai dakin El-Rufai

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164