Yadda na ƙi yarda Boko Haram ta yi sanadin rufe UNIMAID, Farfesa Ibrahim

Yadda na ƙi yarda Boko Haram ta yi sanadin rufe UNIMAID, Farfesa Ibrahim

  • Farfesa Ibrahim Njodi, SSG na jihar Borno ya bayyana kallubalen da ya fuskanta lokacin yana shugaban Jami'ar Maiduguri, UniMaid
  • Tsohon shugaban jami'ar ya ce an bashi zabin rufe makarantar ko kuma cigaba da karatu amma ya ce ba za a rufe ba duk da hare-haren Boko Haram a yankin
  • Sakataren gwamnnatin na jihar Borno ya ce wannan jajircewa da jarumtar da ya yi ta saka gwamnatin tarayya ta bashi lambar yabo

Sakataren gwamnatin jihar Borno, SSG, Farfesa Ibrahim Njodi, ya bayyana yadda ya jajirce ya kammala wa'adinsa a matsayin shugaban jami'ar Maiduguri, UniMaid, ba tare da rufe makarantar ba duk da matsalar Boko Haram a Arewa maso Gabas, rahoton The Punch.

Njodi, kafin nadinsa a matsayin SSG, shine shugaban UniMaid, ya ce ya zabi a cigaba da karatu a jami'ar ba tare da tsoron barazanar hare-haren yan ta'addan ba.

Jami'ar Maiduguri, UniMaid
Kofar shiga Jami'ar Maiduguri, UniMaid. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An kama hatsabibin ɓarawon da ya yi sata gidaje fiye da 1,000 a Kano

A cewarsa, yana da zabin a rufe jami'ar ko kuma a bar ta a bude amma ya zabi a cigaba da karatun.

The Punch ta ruwaito cewa tsohon malamin jami'an wanda aka nada shi shugabanta a ranar 3 ga watan Yunin 2014, ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wurin taron nada shi 'Mayegun' wato jakadar zaman lafiya da kungiyar Oodua Youth Parliament ta yi.

Njodi ya ce, "Na tsaya tsayin daka na ce ba za a rufe Jami'ar Maiduguri ba sai dai Boko Haram ta yi duk abin da za ta yi.

"Gwamnatin tarayya ta karrama mu, hakan yasa aka bani lambar yabo na 'jajircewa wurin aiki na kasa'. Abubuwa sun canja amma kada ka ji tsoro."

KU KARANTA: Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

Yayin da ya ke jinjinawa matasan Nigeria saboda hadin kai da zaman lafiya a kasar, SSG din ya ce dattijai ne ke nuna kiyayya da rashin son zaman lafiya.

A bangarensa, shugaban kungiyar na Oodua Youth Parliament, Abdulmajeed Oyeniyi ya ce kungiyar matasar ta karrama SSG din ne saboda irin jagoranci na gari da ya yi yayin shugabancin jami'ar.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel