Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

  • Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya ce rundunar sojoji ba ta da sauran uzuri kan yaki da ta'addanci
  • Ndume ya bayyana hakan ne sakamakon sabon kasafin kudi na N895 biliyan da Shugaba Buhari ya gabatarwa majalisa don siyo wa sojoji kayan yaki
  • Sanata Ndume ya ce dama ya dade yana neman a kara wa sojojin kudade don su siyo makamai yanzu kuma Shugaba Buhari ya bada kudaden

Shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattijan Nigeria, Sanata Ali Ndume ya ce sojoji ba su da wani sauran uzuri game da yaki da yan ta'adda a yankin Arewa maso gabas da wasu wurare, rahoton Daily Trust.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Ndume ya yi wannan furucin ne cikin jawabin da ya yi a ranar bikin demokradiyya na wannan shekarar.

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno
Shugaban kwamitin sojoji na Majalisar Tarayya, Sanata Ali Ndume. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria sun sace mutane da dama

A makon da ta gabata, majalisar zartarwa na kasa, FEC, ta sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya mika kasafin kudi na Naira biliyan 895 ga Majalisar Tarayya.

Shugaban majalisar Ahmad Lawan ya ce fiye da Naira biliyan 700 daga cikin Biliyan 895 zai tafi ne a bangaren tsaro wurin magance kallubalen tsaron da ake fama da shi yana mai cewa majalisar za ta yi gaggawar amincewa da fitar da kudaden.

A cikin sanarwarsa, Ndume ya ce kudaden za su taimaka wurin yaki da yan ta'adda a kasar.

"A kan batun rashin tsaro, na dade ina neman a kara wa sojoji kudi yanzu kuma an yi hakan ta hanyar kasafin kudin da gwamnati ta gabatar na fiye da Naira biliyan 800 wanda galibin kudin na bangaren tsaro ne. Abin a yaba wa shugaba Buhari ne.

KU KARANTA: Sojojin Nigeria na buƙatar addu'a domin yin nasara kan Boko Haram, Janar na Sojoji

"Da wannan, akwai alamun ana daf da samun nasara domin da zarar an siyo makamai da sauran kayan yaki da sojoji ke bukata aka kuma mika musu. Na tabbata rundunar sojojin Nigeria da aka sani da jarumta za su iya magance kallubalen tsaro da ake fama da shi a Nigeria," in ji shi.

Kada a biya kudin fansa idan masu garkuwa sun sace ni, Mai dakin El-Rufai

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164