Gwamna Ganduje ya magantu kan batun yin ritayarsa daga siyasa

Gwamna Ganduje ya magantu kan batun yin ritayarsa daga siyasa

  • Gwamnan jihar Kano Ganduje ya magantu kan yaushe zai yi ritaya daga harkokin siyasa
  • Ya bayyana cewa, wannan lamari ne na lokaci, idan lokaci ya yi zai dakata amma ba yanzu ba
  • Ya kuma shaida cewa, shi tsohon dan siyasa ne domin ya fara harkar siyasa tun shekarar 1978

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce mai yiwuwa ba zai yi ritaya daga siyasa ba nan kusa, duk da cewa ya shiga siyasa tun 1978, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a yayin wata tattaunawa da mambobin kungiyar 'yan jarida ta Kano a gidan gwamnati.

KU KARANTA: Muna cikin tsaka mai wuya duk da sojojin dake Zaria, Sarkin Zazzau ya koka

Gwamna Ganduje ya yi bayani kan yin ritayarsa daga siyasa
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne biyo bayan sanarwar da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, wanda ya bayyana zai fice daga siyasa a shekarar 2023, Nigeria Tribune ta ruwaito.

A nasa martanin, Mista Ganduje ya ce lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

“A yanzu, ban gaji ba. Ko na yi ritaya ko kada na yi, lokaci zai nuna. Bari in fada muku cewa na shiga siyasa tun shekarar 1978.

"Don haka, ko da na ce zan yi ritaya, idanuna za su ci gaba da kallo, kuma kunnuwana za su ci gaba da ji," in ji shi.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya hana tara 'yan daban siyasa a wuraren taruka a fadin jihar Kano.

Ganduje, wanda ya sanar da dakatarwar ne ta bakin Babban Sakatarensa na yada labarai, Abba Anwar, a cikin wata sanarwa a karshen mako, Punch ta ruwaito.

Ya ce shawarar ta biyo bayan makamai da suka hada da sanduna, takubba, wukake da adduna da 'yan daba suka rike a yayin wani taron a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.