Muna cikin tsaka mai wuya duk da sojojin dake Zaria, Sarkin Zazzau ya koka

Muna cikin tsaka mai wuya duk da sojojin dake Zaria, Sarkin Zazzau ya koka

  • Sarkin Zazzau ya bayyana tsoronsa ga garin Zaria ganin yadda sace-sace ya yawaita a yankin
  • Sarkin ya ce, alamu na nuna garin na cikin mamayar 'yan ta'adda duk da tsaron dake cikinsa
  • Hakazalika ya roki gwamnati da ta dauki matakai wajen ganin an kare jihar daga mamayar

Daily Trust ta ruwaito Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, a ranar Litinin yana cewa garin Zaria na cikin mamayar 'yan ta'adda.

A cewarsa, mazauna garin ba sa iya bacci saboda sace-sacen mutane da ke gudana a tsakanin garin Zariya da kewaye.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, Sarkin ya bayyana lamarin a matsayin abinda ba za a yarda da shi ba don haka ya bukaci gwamnati ta dauki mataki.

KU KARANTA: Tambuwal Ga ’Yan Najeriya: Ku Taya Mu da Addu’a, PDP Na Tsara Karbe Mulki a 2023

Garin Zaria na kewaye da 'yan ta'adda, sarkin Zazzau ya bayyana
Sarkin Zazzau, Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin wasu shugabannin tsaro karkashin jagorancin Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan.

Sarkin ya ce akwai tsare-tsaren tsaro da makarantun horar da sojoji a cikin garin amma sam mutanensa ba sa cikin kwanciyar hankali.

A nasa bangaren, Samuel Aruwan ya ce sun je fadar ne domin karfafa gwiwa da kuma mika ta'aziyyarsu ga masarautar kan mummunan lamarin da ya faru a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da sauran makwabta, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin jihar tana yin duk mai yiwuwa don kare masarautar da jihar baki daya.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya da Manoma: Makiyaya Sun Sare Hannun Wani Manomi a Yayin Rikici

A wani labarin, Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yanke hannun dama na wani manomin shinkafa mai suna Saheed Zakariyau, a kauyen Bindofu dake masarautar Lafiagi, a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, Punch ta ruwaito.

Manomin, a cewar majiyoyi, ana zargin an kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Bindofu a ranar Asabar da ta gabata bayan ya zargi makiyayan da ingiza dabbobinsu wajen lalata gonarsa.

An tattaro cewa wanda manomin, tare da abokan aikinsa, ya je gonar a ranar Asabar kuma ya gano cewa makiyayan sun yi kiwon shanunsu a gonarsa tare da lalata amfanin gonar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel