Ganduje: Zan Yi Maganin Duk Dan Siyasar da Ke Son Bata Siyasarmu Da ’Yan Daba
- Gwamnan jihar Kano ya bayyana hana taron siyasar da zai gayyato 'yan daba a wajen taro
- A cewarsa, zai yi maganin duk wani dan siyasar da ya taka wannan doka da ya sanya yanzu
- Ya kuma bayyana tsaftar siyasar jihar Kano, yana mai cewa siyasar Kano ta ilimi ce da hankali
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya hana tara 'yan daban siyasa a wuraren taruka a fadin jihar Kano.
Ganduje, wanda ya sanar da dakatarwar ne ta bakin Babban Sakatarensa na yada labarai, Abba Anwar, a cikin wata sanarwa a karshen mako, Punch ta ruwaito.
Ya ce shawarar ta biyo bayan makamai da suka hada da sanduna, takubba, wukake da adduna da 'yan daba suka rike a yayin wani taron a Kano.
KU KARANTA: NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba, ta bayyana mafita
“Ba za mu yarda da wannan ba kuma ina tabbatar muku cewa zan yi maganin duk wani dan siyasa da ya karya wannan gargadin.
“A yayin bikin kaddamar da hanyar Kano-Gwarzo-Dayi, a wannar rana, 'yan daban siyasa sun nuna cikin halaye marasa kyau.
“Na sanar da ku cewa muna bikin ranar Dimokiradiyya, tare da jerin abubuwan da za su tabbatar da kasancewar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Gwamnan Jihar Yobe, da sauransu.
“A dalilin wannan, jam’iyyar tana sanar da hana dukkan wani nau’i na kamfen ga kowane dan siyasa yayin taron.
“Ni da kaina zan ba da umarnin kamawa tare da hukunta duk wanda aka kama yana safarar makamai a lokacin.
The Nation ta ruwaito gwamnan yana yaba siyasar jihar Kano, tare da bayyana tsaftar inda yake cewa:"Siyasarmu a Kano ta dogara ne da kyakkyawan tunani da ilimi, mai da hankali kan kyawawan manufofi ba wai na rashin kulawa da hauka ba."
KU KARANTA: Manjo Hamza Al-Mustapha Ya Ba Shugaban Hafsan Soji Shawari Kan Yaki da Boko Haram
A wani labarin, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya tabbatar da tsige Cif Letep Dabang a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Punch ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren Asabar yayin wata liyafar cin abincin dare da aka shirya ta masu ruwa da tsaki a matsayin wani bangare na ayyukan bikin ranar Dimokiradiyya ta 12 ga Yuni wanda aka gudanar a gidan Gwamnatin Rayfield da ke Jos.
Lalong a jawabinsa ya gabatar da sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar in da yake cewa:
“Muna da sabon shugaban jam'iyyar APC a Filato. Yana nan tare da mu. Na gan shi yana kokarin aika sakon tes ta hanyar amfani da wayarsa na ce, bari na tsaya a nan na gabatar dashi kafin ya bace mani.”
Asali: Legit.ng