Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi

Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi

  • Gwamnonin a karkashin jam'iyyar PDP sun koka kan yadda gwamnatin Buhari ke cin bashi
  • Gwamnonin sun ce hakan ya saba wa tsarin mulkin kasa, kuma zai iya ruguza tattalin arzikin Najeriya
  • Sun kuma koka kan yadda CBN ke gudanar da ayyukanta, ciki har da kirkirar kudade da kashe su

Gwamnoni a karkashin jam'iyyar PDP a ranar Litinin sun gabatar da kararraki kan kudin da jam'iyyar APC karkashin mulkin shugaba Buhari ke karba bashi don gudanar da ayyuka a kasar, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan wani bangare ne na kudurorin da aka cimma a karshen taron kungiyar gwamnonin PDP da aka gudanar a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

“Ya kamata a ranto kudi saboda dalilai masu amfani, bashin da ake bin Najeriya a yanzu na sama da Naira tiriliyan 36 ya bayyana a fili mara amfani mai dorewa ga kudin shigar mu da GDP.

KU KARANTA: Muna cikin tsaka mai wuya duk da sojojin dake Zaria, Sarkin Zazzau ya koka

Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi
Gwamnonin jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Bai kamata mu dora wa karni masu zuwa nauyin bashi ba. Bashin da gwamnatin APC ke ci idan ba a yi hankali ba zai kai Najeriya ga fatarar rugujewa, ”sanarwar da aka fitar a karshen taron ta karanto wani sashi.

Gwamnonin sun yi Allah-wadai da cewa bashin da ake bin Najeriya tare da sama da 80% na alawus din da aka kashe wajen biyan bashi yana ta kara hauhawa kuma ya zama abinda ba za a iya shawo kansa ba.

Sun bayyana cewa duk nasarorin da gwamnatin PDP ta samu a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo lokacin da kasar ta fita daga bashin da kasashen waje ke bin ta duk yanzu ya rushe.

Gwamnonin sun zargi wannan gwamnati da karbar bashi don wasu abubuwa marasa kyau, suna masu jaddada cewa irin wannan matakin abin kunya ne.

Gwamnonin PDP sun yi watsi da tsarukan CBN da ayyukanta

Legit ta gano cewa, gwamnonin sun y watsi da tsarin aiki na Babban Bankin Najeriya (CBN) wanda suke ikirarin suna aiki ne a matsayin gwamnati mai zaman kanta-a cikin-gwamnati.

“Yanayin da CBN ke kirkirar kudi, ta yanke shawarin nawa za a kashe, a kan abin da za a kashe shi ba tare da wani tsari na sarrafawa ko sa ido ba hakan ya saba wa tsarin mulkinmu.

KU KARANTA: JAMB Ta Fidda Sabuwar Sanarwa Kan Ranar Rufe Rajistar Jarrabawar Shekarar 2021

A wani labarin, Gwamnonin da ke karkashin jam'iyyar PDP sun hadu a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom don yin shawarwari kan yadda za a tumbuke jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023, Premium Times ta ruwaito.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, gwamnonin suka yi alkawarin samar da tsarin da jam'iyyar ke bukata don dawowa kan mulki a matakin tarayya a 2023

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya yi wannan alkawarin a wata liyafa da gwamnatin jihar Akwa-lbom ta shirya, gabanin taron kungiyar a Uyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.