Jerin manyan yan Najeriya 4 da ‘yan bindiga suka kashe cikin kwanaki uku da suka gabata

Jerin manyan yan Najeriya 4 da ‘yan bindiga suka kashe cikin kwanaki uku da suka gabata

Yayin da rashin tsaro ya yi kamari a cikin kasar, wasu fitattun 'yan Najeriya sun rasa rayukansu sakamakon harbe su da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi.

Legit.ng ta kawo maku jerin manyan yan Najeriya, wasu yan kasuwa da kuma yan siyasan da ‘yan bindiga suka kashe a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Mazauna garin Gauraka na jihar Neja sun tsere sun bar gidajensu yayinda aka ceto mutum 20 da aka sace

Jerin manyan yan Najeriya 4 da ‘yan bindiga suka kashe cikin kwanaki uku da suka gabata
Jerin manyan yan Najeriya 4 da ‘yan bindiga suka kashe cikin kwanaki uku da suka gabata Hoto: bbc.com
Asali: UGC

1. Ahmed Gulak

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Gulak, jigo a jam'iyyar All Progresive Congress, APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a ranar Lahadi lokacin da yan bindigan suka kashe shi.

2. Justice Stanley Nnaji

A daren ranar Lahadi ne wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka kashe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu, Justice Stanley Nnaji, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Nnaji, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Isi-Uzo, an harbe shi ne a kusa da wata cibiyar binciken cututtuka, lokacin da maharan suka tare shi suka fito dashi daga cikin motarsa.

Da yake tabbatar da kisan, kwamishinan yan sandan jihar Enugu, Mohammed Ndatsu Aliyu, yace ya ƙaddamar da bincike kan maharan da ba'a san ko su waye ba, waɗanda suka yi awon gaba da motar mamacin.

3. Linus Owuamanam

A ranar Asabar da daddare ne wasu yan bindiga da ba'a gano ko su waye ba sun harbe wani ɗan kasuwa, Linus Owuamanam, har lahira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan kasuwan mai suna, Linus Owuamanam, yana cikin tuƙa motar bas yayin da lamarin ya faru dashi a kan hanyar Mokola-Sango Ibadan, jihar Oyo.

KU KARANTA KUMA: Ana zanga zanga a jihohin Najeriya hudu kan rashin tsaro da rashin shugabanci mai inganci

4. Okiemute Mrere

Hakazalika a ranar Asabar ne yan bindiga suka halaka shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, reshen jihar Imo, Okiemute Mrere.

An kashe Mrere a kan babban titin Owerri zuwa Fatakwal dake Owerri, The Punch ta gano hakan a ranar Litinin.

Babban jami'in hukumar ya tabbatar da hakan inda yace an ga gawar shugaban a daji da safiyar Lahadi.

A wani labarin, majalisar dattijai a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dunga tunawa da marigayi Babban Hafsan Sojojin kasar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Hakanan majalisar ta yi shiru na minti guda don girmama mamacin.

Wannan ya biyo bayan wani oda da shugaban kwamitin majalisar dattijai kan Soja, Sanata Ali Ndume ya gabatar, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel