A ƙarshe dan Gulak ya magantu, ya bayyana kalmomin mahaifinsa na ƙarshe

A ƙarshe dan Gulak ya magantu, ya bayyana kalmomin mahaifinsa na ƙarshe

- Mohammed, daya daga cikin ‘ya’yan tsohon hadimin tsohon shugaban kasar da aka kashe, Ahmed Gulak, ya bayyana yadda iyalan suka samu wannan labari na bakin ciki

- Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe Gulak a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, a Owerri, babban birnin jihar Imo a hanyar sa ta zuwa filin jirgin sama

- A cewarsa, mahaifinsa ya rasu ne a Owerri don shirin sake duba kundin tsarin mulki da mambobin majalisar ke yi

Kasa da sa’o’i 24 bayan kashe mahaifinsa a Imo, Mohammed, dan Ahmed Gulak, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce marigayin ya ziyarci jihar a matsayin mamba na kwamitin sake duba kundin tsarin mulki.

Legit.ng ta rahoto cewa an kashe Gulak, wani jigo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, a Owerri, babban birnin jihar Imo.

KU KARANTA KUMA: Harkoki sun tsaya cak yayinda mazauna wasu jihohin kudu ke bin umarnin zaman gida

A ƙarshe dan Gulak ya magantu, ya bayyana kalmomin mahaifinsa na ƙarshe
A ƙarshe dan Gulak ya magantu, ya bayyana kalmomin mahaifinsa na ƙarshe Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

An tattaro cewa mamacin shine shugaban kwamitin APC wanda ya gudanar da zaben fidda gwani na zaben gwamnan Imo a 2019.

Hadimin mahaifina ne ya sanar da mu mummunan labarin

Mohammed, wanda ya shaida wa BBC Pidgin kan lamarin, ya ce yana cikin dakinsa a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, yana jiran direban da zai kai su filin jirgin sama don tarbar mahaifinsa kafin labarin harbin ya bayyana.

Ya kara da cewa hadimin mamacin shi ne mutum na farko da ya kira iyalin ta wayar tarho ya tambaye su ko sun ji abin da ya faru sannan kuma ya katse kiran lokacin da amsar ya sha bambam.

Dan Gulak ya kuma bayyana cewa babban cikinsu ne ya sanar da labarin ga iyalin lokacin da ya shiga gidan cikin zubar hawaye.

Ya ce:

"A safiyar Lahadi, ina cikin dakina ina jiran direbansa (Gulak) ya zo don mu tafi filin jirgin sama don dawo da shi gida."
“Mataimakin mahaifinmu ne ya fara kira ta wayar tarho ya tambaye mu ko mun ji abin da ya faru. Da muka ce ‘a’a’, sai ya katse kiran. Wataƙila bai so ya gaya mana wannan labarin ba.
“Bayan‘ yan mintoci, sai babban yayanmu ya shigo gidan yana kuka sai ya gaya mana labarin mutuwar mahaifinmu. Abu na farko da na fara yi shi ne kiran layin wayarsa don tabbatarwa kuma ba ta shiga ba. Bayan haka, kowa a cikin gidan ya fara kuka.''

KU KARANTA KUMA: Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa

Gulak na daga cikin kwamiti kan nazarin kundin tsarin mulki da ke gudana

Da yake magana a kan abin da ya kai Gulak Imo, ya bayyana cewa marigayin yana cikin kwamitin da ke nazari kan sake fasalin kundin tsarin mulki.

Mohammed ya bayyana kalaman Gulak na karshe a gareshi

A cewarsa, hirarsa ta karshe da mahaifinsa wani abu ne da ba zai taba mantawa da shi ba a rayuwarsa.

Mohammed ya ce:

“A ranar Asabar, na kira shi da karfe 8 na dare don gaishe shi kuma na yi masa addu’ar dawowa gida lafiya washegari. Ya yi farin ciki sannan ya ce mini ‘Allah ya albarkace ka, ɗana. Yana daga cikin kwamiti kan nazarin kudin tsarin mulki. Ya je Owerri don gudanar da aikin.”

A wani labarin, tohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana jimaminsa game da kashe Ahmed Gulak, tsohon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa.

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Gulak a yayin da yake komawa Abuja daga Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar Lahadi, TheCable ta ruwaito.

Da yake maida martani game da labarin, Jonathan ya yaba wa marigayin a matsayin "mai yi wa kasa hidima mai aminci", yana mai bayyana yadda yaji zafin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel