Jonathan Ya Yi Jimamin Mutuwar Ahmed Gulak, Ya Yi Martani Game Dashi

Jonathan Ya Yi Jimamin Mutuwar Ahmed Gulak, Ya Yi Martani Game Dashi

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi martani kan kisan tsohon hadiminsa Ahmed Gulak

- Ya bayyana Gulak a matsayin dan kasa mai kishi, sannan kuma mai aiki tukuru da jajircewa

- Ya mika ta'aziyya ga 'yan uwa, abokai da ilahirin jama'ar jihar Adamawa da Najeriya kan babban rashin

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana jimaminsa game da kashe Ahmed Gulak, tsohon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa.

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Gulak a yayin da yake komawa Abuja daga Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar Lahadi, TheCable ta ruwaito.

Da yake maida martani game da labarin, Jonathan ya yaba wa marigayin a matsayin "mai yi wa kasa hidima mai aminci", yana mai bayyana yadda yaji zafin mutuwarsa.

KU KARANTA: Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

Jonathan Ya Yi Jimamin Mutuwar Ahmed Gulak, Ya Yi Martani Game Dashi
Jonathan Ya Yi Jimamin Mutuwar Ahmed Gulak, Ya Yi Martani Game Dashi Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ikechukwu Eze, mai ba da shawari na musamman kan harkokin yada labarai ga tsohon shugaban ne ya fitar da sanarwar.

Sanarwar ta karanta: “Na shiga matukar damuwa da mutuwar Alh Ahmed Gulak wanda ya mutu a ranar Lahadi, 30 ga Mayu, 2021, a Owerri, Jihar Imo.

“Gulak ya kasance ma'aikacin gwamnati mai yiwa kasa hidima kuma mai kishin kasa wanda ya sadaukar da komai nasa don yi wa kasarsa aiki. Mutuwarsa rashi ne mai radadi a wurina da sauran mutane da yawa wadanda suka yi aiki tare da shi.

"Za a tuna da shi saboda irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban dimokuradiyyar kasarmu, musamman ma ranakun da ba za a manta da su ba a matsayinsa na kwararren kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa kuma mai ba da shawara kan harkokin siyasa a gwamnatinmu."

Jonathan ya mika ta’aziyyarsa ga dangin Gulak, gwamnati da kuma al’ummar jihar Adamawa, wadanda za su ji zafin rashin wannan fitaccen mai kishin kasa Najeriya, PM News ta ruwaito.

KU KARANTA: Kungiyar 'Yan Tawaye Ta IPOB Ta Yi Martani Kan Zarginta Da Kashe Ahmed Gulak

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wadanda ke da alhakin mutuwar dan siyasar Adamawa, Ahmed Gulak, ba za su tafi ba tare da an hukunta su ba.

An kashe Gulak a jihar Imo yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a ranar Lahadi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasan kasa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce lallai ya girgiza kumaya kyamaci abinda aka aikatawa marigayin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel