Harkoki sun tsaya cak yayinda mazauna wasu jihohin kudu ke bin umarnin zaman gida

Harkoki sun tsaya cak yayinda mazauna wasu jihohin kudu ke bin umarnin zaman gida

- Shaguna da makarantu da sauran wurare sun kasance a rufe a wasu yankuna na jihohin kudu maso gabashin Najeriya sakamakon umarnin da kungiyar IPOB ta bayar na a zauna a gida

- Kungiyar ta umarci mazauna yankunan da su kasance a gida daga yau Litinin don bikin cika shekara 54 da gama yaƙin basasarar Biafra

- Sai dai kuma, akwai jami'an tsaro da yawa a wurare masu mahimmanci don hana karya doka da oda

Harkokin tattalin arziki da kasuwanci sun tsaya cak a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, a yankin Kudu Maso Gabashin ƙasar, gidan talbijin na Channels ta ruwaito.

Wannan ya yi daidai da umarnin zaman gida da haramtacciyar kungiyar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB) ta bayar.

IPOB, ta bakin kakakinta, Emma Powerful ta ce za a takaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa a duk yankin Kudu maso Gabas a ranar Litinin don bikin cika shekaru 54 da gama yaƙin basasarar Biafra.

Harkoki sun tsaya cak yayinda mazauna wasu jihohin kudu ke bin umarnin zaman gida
Harkoki sun tsaya cak yayinda mazauna wasu jihohin kudu ke bin umarnin zaman gida Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A kan haka, titunan cikin Owerri, babban birnin jihar Imo sun zama fanko. Harkokin kasuwanci, makarantu, da sauran manyan cibiyoyin tattalin arziki sun kasance a rufe. An kuma tsayar da zirga-zirgar ababen hawa.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Mutane da dama sun jikkata yayinda abun fashewa ya tashi a kasuwar Port Harcourt

Sai dai kumA, akwai jami'an tsaro da yawa a wurare masu mahimmanci a cikin birni don hana karya doka da oda.

A jihar Abia, tituna sun kasance ba kowa kuma shaguna suna kulle yayin da a jihar Anambra, lamarin daya ne. An dakatar da ayyukan tattalin arziki da zamantakewar al'umma kuma akwai tsaro sosai a manyan wurare na jihar don kiyaye doka da oda.

Gwamna Okezie Ikpeazu a daren Lahadi, ya ce ba za a tilasta wa ‘yan kasuwar na Abia bude shagunansu ba idan suka zabi rashin zama a gida, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin bai bambanta ba sosai a jihar Ebonyi saboda an ga motoci kalilan a babbar hanya. Titunan unguwanni sun kasance ba kowa tare da jami'an tsaro da aka sanya su a wurare daban-daban.

Yawancin kasuwanni a babban birnin jihar Delta, Asaba sun kasance a rufe saboda mazauna suna bin umarnin zaman gida. Bankuna da manyan wuraren kasuwanci sun kasance a rufe.

KU KARANTA KUMA: Matasan Zamfara sun toshe babbar hanya, sun lalata ababen hawa a wata mummunar zanga-zanga da suke gudanarwa

A wani labarin na daban, 'Yan sanda a babban birnin Tarayya Abuja sun harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon dan takarar shugaban kasa yayin wata zanga-zanga a bakin Unity Fountain dake a Abuja.

An harbi Sowore a gefen dama a cinya lamarin da ya sa aka yi gaggawan wucewa dashi asibiti.

Ya rubuta a shafin Tuwita: "Yanzun nan 'yar sanda, ACP Atine ta harbe ni a Unity Fountain a Abuja. #RevolutionNow Yanzu aka fara gwagwarmaya za ta ci gaba koda kuwa za su dauki raina!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel