Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

- Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr Isa Pantami, yace za'a samar da cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) akalla ɗaya a kowace jiha

- Ministan yace a halin yanzun ma'aikatarsa ta ƙaddamar da ECC 23 a faɗin ƙasar nan kuma akwai sauran 13 dake tafe

- Yace ECC zata taimaka wa yan Najeriya wajen isar da sako cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da an caje su kuɗi ba

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami, ya bayyana shirinsa na samar da aƙalla cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) ɗaya a kowace jiha kafin ƙarewar 2022, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: NCS: Hameed Ali Ya Kafa Sabon Tarihi, Ƴa Samar da Biliyan N799bn Cikin Watanni 5

Ministan ya faɗi haka ne a wajen ƙaddamar da sabon tsarin tattalin arziƙin zamani rukuni na 10 a babban birnin tarayya Abuja.

Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Sadarwa Ta Gaggawa Kafin 2022, Sheikh Pantami
Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Sadarwa Ta Gaggawa Kafin 2022, Sheikh Pantami Hoto: @FMoCDENigeria
Asali: Twitter

A cewar Pantami, an ƙaddamar da ECC 23 a faɗin Najeriya, kuma akwai ragowar 13 da ake cikin aikin su.

Rahoton BBC ya nuna cewa tuni ministan ya buɗe ofishin farko a wannan tsarin a jihar Katsina matakin da ya bai wa sama da mutum 40 aikin yi.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi: Ɗumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Jami'ar Jihar Taraba, Sun Yi Awon Gaba da Malami

Yace: "A cikin shekaru biyu, mun buɗe sabbin Cibiyoyin amsa kiran gaggawa 23 a faɗin Najeriya, kuma kawai sauran 13 dake tafe."

"Tsarin da muka yi shine a samar da aƙalla ECC ɗaya a kowacce jiha dake faɗin Najeriya kafin ƙarshen shekarar 2022."

"Waɗannan cibiyoyin suna da matuƙar amfani, Lamba ce da zakai amfani ita kyauta, idan ka kira lambar ba za'a caje ka ko sisi ba."

Pantami ya kara da cewa wannan tsarin zai taimaka wa yan Najeriya wajen bada haɗin kai da taimaka musu wajen isar da saƙon gaggawa musamman akan tsaro.

A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu

Wasu yan bindiga sun harbe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu har Lahira ranar Lahadi da daddare.

Rahotanni Sun bayyana cewa maharan sun tare alƙalin ne a kan hanya yana cikin tafiya a mota, sannan suka aikata mummunan nufin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262