NCS: Hameed Ali Ya Kafa Sabon Tarihi, Ƴa Samar da Biliyan N799bn Cikin Watanni 5
- Hukumar kwastam ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Hameed Ali ta kafa sabon tarihi na samar da kuɗin shiga ga gwamnati
- A karo na farko NCS ta samar da kuɗaɗen shiga kimanin biliyan N799bn a cikin watanni biyar kacal
- Kakakin hukumar kwastam na ƙasa, Joseph Attah, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja
Hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) ta samar da kuɗi kimanin biliyan N799bn na kuɗaɗen shiga daga watan Janairu zuwa Mayu 2021, karon farko a tarihin hukumar, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi: Ɗumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Jami'ar Jihar Taraba, Sun Yi Awon Gaba da Malami
Kakakin NCS, Joseph Attah, shine ya bayyana haka ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.
Mr Attah yace wannan adadin ya zarce abinda hukumar ta samar a irin wannan lokacin a shekarar data gabata 2020.
Ya ƙara da cewa hukumar ta samu wannan nasara ne saboda zartad da dukkan wata doka ta shige da ficen kayayyaki a fadin ƙasar nan.
Attah yace dabarun canza wa jami'an hukumar wurin aiki da kuma cigaba da yin hakan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa hukumar ta cimma wannan nasara.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu
A cewarsa, ƙara wa jami'an NCS ƙarfin guiwa su saka ƙasar su a gaba fiye da buƙatunsu na daga cikin abinda yasa kuɗaɗen shigan suka ƙaru.
Yace wasu dalilan sun haɗa da, ƙarin samun haɗin kai da aka samu daga masu faɗa aji na ƙasar nan da kuma kyakkyawar alaƙa tsakanin NCS da yan majalisun ƙasar nan.
Kakakin NCS ɗin ya ƙara da cewa: "Hukumar kwastam ƙarƙashin jagorancin Hameed Ali zata cigaba da ɓullo da sabbin dabaru waɗanda zasu taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da tsaro."
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu
Rundunar yan sandan jihar Imo, ta bayyana cewa ta gano waɗanda suka kashe Ahmed Gulak, kamae yadda Premium Times ta ruwaito.
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abutu Yaro, shine ya bayyana haka a wani jawabi da rundunar ta fitar ɗauke da sa hannunsa.
Asali: Legit.ng