Da Ɗumi: Ɗumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Jami'ar Jihar Taraba, Sun Yi Awon Gaba da Malami

Da Ɗumi: Ɗumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Jami'ar Jihar Taraba, Sun Yi Awon Gaba da Malami

- Wasu yan bindiga sun kutsa kai gidajen kwanan malaman jami'ar jihar Taraba, inda suka sace wani lakcara

- Shugaban Makarantar (VC), Farfesa Ado-Tenebe ya tabbatar da faruwar lamarin, yace yayi matuƙar mamaki yadda akai haka ta faru a jami'arsa

- Ya ƙara da cewa zasu cigaba da ɗaukar matakan duk da ya kamata domin ganin an magance faruwar irin haka nan gaba

Wasu yan bindiga sun kutsa kai cikin jami'a sun yi awon gaba da malami a gidajen kwanan malamai a jami'ar jihar Taraba dake Jalingo, babban birnin jihar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu

Lakcaran mai suna, Umar Buba, shugaban sashin koyar da ilimin gandun daji, an sace shi ne da safiyar Lahadi a cewar shugaban jami'ar, farfesa Vincent Ado-Tenebe.

Ado-Tenebe, wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, yace maharan sun yi harbi a sama domin tsoratar da jami'an tsaron dake gadi a wajen.

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sake Kutsawa Jami'a, Su Yi Awon Gaba da Lakcara
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sake Kutsawa Jami'a, Su Yi Awon Gaba da Lakcara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace: "Wannan labari ne mara daɗi, kuma bai taɓa faruwa ba shekaru 2-3 da suka wuce, tun sanda aka ɗauke daraktan yaɗa labarai."

"Nayi matuƙar mamaki da haka ta sake faruwa a jami'ar mu sabida matakan da muka ɗauka tun bayan faruwar wancan lamarin. Nasan muna da jami'an yan sanda, jami'an NSCDC, da jami'an sa kai da muka ɗauka domin su kare mu daga irin wannan harin."

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu

Shugaban makarantar ya bada tabbacin za'a yi iya bakin ƙoƙarin da ya kamata wajen ganin an ƙaro jami'an tsaro, da kuma buƙatar kayan aiki ga jami'an domin yaƙar yan ta'addan.

Yace ma'aikatan makarantar da ɗalibai ba zasu iya tunkarar yan bindiga da hannun su ba, ya ƙara da cewa hukumar makarantar zata duba yuwuwar yadda za'ayi ma'aikata su mallaki bindiga bisa doka domin kare kan su.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa Tare da Wasu Mutum Uku

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wani ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa a kan hanyarsa ta zuwa Jos.

Shugaban kwamitin hulɗa da jama'a na majalisar, Hon Mohammed Omadefu, shine ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262