Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu
- Wasu yan bindiga sun harbe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu har Lahira ranar Lahadi da daddare
- Rahotanni Sun bayyana cewa maharan sun tare alƙalin ne a kan hanya yana cikin tafiya a mota, sannan suka aikata mummunan nufin su
- Kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar da cewa zasu binciko waɗanda suka aikata wannan kisan duk inda suke
Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kashe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu, Justice Stanley Nnaji, ranar Lahadi da daddare, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Gwamnan Neja Ya Shilla Ƙasar Waje Tare da Matarsa Bayan Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Islamiyya a Jiharsa
Nnaji, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Isi-Uzo, an harbe shi ne a kusa da wata cibiyar binciken cututtuka, lokacin da maharan suka tare shi suka fito dashi daga cikin motarsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Da yake tabbatar da kisan, kwamishinan yan sandan jihar Enugu, Mohammed Ndatsu Aliyu, yace ya ƙaddamar da bincike kan maharan da ba'a san ko su waye ba, waɗanda suka yi awon gaba da motar mamacin.
A jawabin da kakakin rundunar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya fitar, kwamishinan yace an gaggauta kai alƙalin asibiti, inda likita ya tabbatar da rai yayi halinsa.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu
Ya kuma ƙara da cewa a yanzun haka an ajiye gawar mamacin a ɗakin ajiye gawa dake asibiti.
Yace: "Ina tabbatar da cewa ba zamu bar wannan lamarin ya wuce hakanan ba, zamu binciko duk masu hannu a kan wannan kisan."
"Ina kira ga mazauna jihar Enugu da su cigaba da bin doka sau da ƙafa, sannan kuma su taimaka wa jami'an yan sanda da bayanai domin ganin an kamo waɗannan yan ta'addan."
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan
Wasu yan bindiga sun harbe wani hamshaƙin ɗan kasuwa har Lahira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Bayan sun harbi mutumin, maharan sun caka masa wuƙa a ƙirji domin su tabbatar bai tsira da ransa ba.
Asali: Legit.ng