Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU Ta Zaɓi Sabon Shugaba
- Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa ASUU ta bayyana sabbon shugaban ta bayan kammala wa'adin farfesa Ogunyemi
- Farfesa Emmanuel Osodeke, shine ƙungiyar ta zaɓa a matsayin sabon shugabanta, wanda shine mataimakin shugaba a baya
- Ƙungiyar ta gudanar da zaɓen ne a yayin wani taron kwana uku da tayi a jami'ar Nnamdi Azikiwe dake jihar Anambra
An bayyana mataimakin shugaban ƙungiyar ASUU, Emmanuel Osodeke, a matsayin Sabon shugaban ƙungiyar bayan kammala wa'adin farfesa Biodun Ogunyemi a satin daya gabata, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa
An zaɓi Mr Osodeke, Farfesa a ɓangaren kimiyyar ƙasa a jami'ar koyon aikin gona, jihar Abia, ranar Lahadi a wajen taron ƙungiyar da ya gudana a jami'ar Nnamdi Azikiwe Awka, jihar Anambra.
Sabon shugaban zai amsa daga hannun Farfesa Biodun Ogunyemi na jami'ar Olabisi Onabanjo dake jihar Ogun, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
Sauran waɗanda aka zaɓa ɗin sun haɗa da: Chris Piwuna daga jami'ar Jos, a matsayin mataimakin shugaba; Olusiji Sowande daga jami'ar koyon aikin gona (FUNAAB), Abekuta, a matsayin ma'ajiyin kudi.
Farfesa Ade Adejumo, daga jami'ar Ladoke Akintola (LUTECH), Ogbomoso, a matsayin sakataren kuɗi;Austen Sado daga jami'ar Patakwal a matsayin sakataren Zuba jari.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa
Sauran sune: Adamu Babayo daga jami'ar Abubakar Tafawa Balewa(ATBU) Bauchi, a matsayin mai bincike, Stella-Maris daga jami'ar kimiyya da fasaha dake jihar Rivers, a matsayin sakataren walwala.
Tsohon shugaba, Mr Ogunyemi, zai cigaba da aiki tare da sabbin shugabannin da aka zaɓa domin taimaka musu wajen jagorancin ƙungiyar.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi
Rundunar yan sanda reshen jihar Kogi ta bayyana cewa ta damƙe wasu mutum huɗu ɗauke da makamai a jihar.
Kakakin hukumar na juhar, William Aya, yace jami'an Operation Puff Ander ne suka kama waɗanda ake zargin.
Asali: Legit.ng