Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa

- Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wani ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa a kan hanyarsa ta zuwa Jos

- Shugaban kwamitin hulɗa da jama'a na majalisar, Hon Mohammed Omadefu, shine ya tabbatar da faruwar lamarin

- Yace yan bindigan sun tuntuɓi majalisar dokoki amma har yanzun ba su nemi a basu kuɗin fansa ba

Wasu yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa, mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta tsakiya, Hon Ismai Danbaba, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi

Rahoton Dailytrust ya bayyaɓa cewa An sace Ɗanbaba ne da yammacin ranar Asabar a kan hanyarsa ta zuwa Jos, jihar Plateau, tare da direbansa da wasu mutum biyu.

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin hulɗa da jama'a na majalisar jihar, Hon Mohammed Omadefu, shine ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ranar Lahadi.

Yace lamarin ya faru ne a dai-dai dajin ƙaramar hukumar Sanga, dake jihar Kaduna.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa

Yace ɗan majalisar ya wuce garin Andaha ƙaramar hukumar Akwanga jihar Nasarawa, inda ya nufi Dajin Sanga, a nan ne yan bindigan suka farmake shi kuma suka yi awon gaba dashi.

Omadefu, wanda ke wakiltar mazaɓar Keana a majalisar dokokin Nasarawa, ƙaraƙashin jam'iyyar APC, yace:

"Yan bindigan sun tuntuɓi majalisar dokokin jihar amma har yanzun basu nemi a basu kuɗin fansa ba."

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sandan jihar Nasarawa, ASP Rahman Nansel, Yace lamarin ba'a jihar Nasarawa ya faru ba saboda haka ba zai iya cewa komai ba.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Gwamnan Rivers, Nyesom Wike , ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 dake tafe.

Wike yace idan yana da muradin tsayawa takara a jam'iyyarsa ta PDP, babu wanda ya isa ya dakatar dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel