Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa

- Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya hana amfani da babur, keke nafef da ƙaramar motar bas a faɗin jiharsa

- Gwamnan yace ɗaukar wannan matakin ya zama wajibi domin inganta tsaron jihar dake ƙara taɓarɓarewa

- Gwamnan ya kuma roƙi matasa da masu ruwa da tsaki a jihar su zama jakadu nagari wajen tabbatar da wannan dokar tayi aiki

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya hana amfani da babur, keke nafef da ƙananan motocin bas a faɗin jihar daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa

Gwamnan ya ɗau wannan matakin ne domin magance matsalar tsaro dake kara taɓarbarewa a jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa Hoto: @WillieMObiano
Asali: Twitter

A wani jawabi da sakataren gwamnatin Anambra, Prof Solo Chukwulobelu, ya fitar, Obiano yace:

"Mun yi wannan hanin ne domin inganta yanayin tsaro a jihar mu, kuma mu dakatar da hare-haren da ake kaiwa a babur, keke nafef da ƙananan motocin bas a faɗin jihar."

A cewar gwamna Obiano, hana amfani da babur a yankunan Onitsha da Awka da gwamnati tayi tun farko yana nan daram.

KARANTA ANAN: Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Yace duk babur ɗin da aka kama a wannan yankunan gwamnati zata ƙwace shi daga hannun ko waye.

Gwamna Obiano, ya roƙi matasa da masu ruwa da tsaki na jihar da su zama jakadun tsaro a yankunan su, su taimaka wa jami'an tsaro wajen tabbatar da an bi wannan doka sau da ƙafa.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar 'Trophée Babacar Ndiaye' Ta Nahiyar Africa 2021

An bayyan shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe lambar yabon "Gwarzon mai gina hanyoyi 2021' wacce akewa laƙabi da Trophée Babacar Ndiaye, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban zai amshi kyautar ne daga hannun takwaransa na ƙasar Egypt, Abdul-Fattah Al-Sisi wanda ya lashe shekarar data gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel