Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi

Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi

- Rundunar yan sanda reshen jihar Kogi ta bayyana cewa ta damƙe wasu mutum huɗu ɗauke da makamai a jihar

- Kakakin hukumar na juhar, William Aya, yace jami'an Operation Puff Ander ne suka kama waɗanda ake zargin

- Yace za'a gurfanar da mutanen a gaban alƙali da zarar an kammala bincike akan su

Rundunar yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ta cafke wasu mutum huɗu da take zargi da mallakar bindigu da alburusai ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda Daily nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa

A wani jawabi da hukumar ta fitar a Lokoja ranar Asabar, tace jami'an Operation Puff Ander ne suka kama waɗanda ake zargin tare da taimakon jami'an caji ofis ɗin Ayara.

Jawabin wanda yake ɗauke da sa hannun kakakin rundunar, William Aya, yace an kama mutanen ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma yayin bincike abun hawa a kan hanyar Iyamoye/Kabba.

Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi
Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

"An kama waɗanda ake zargin ne a cikin motocin hawa biyu lokacin da jami'ai ke gudanar da binciken abun hawa, mutanen sun gaza bayanin yadda suka mallaki makaman." Inji Aya.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa

Aya ya bayyana sunayen mutanen da aka kama ɗin da, Yahaya Yakubu, 53, Ojo Dada, 20, Mohammed Okehi, 31, da kuma Saliu Jimoh, 45.

Hakanan ya bayyana makaman da aka samu tare da su waɗanda suka haɗa da, bindigun gargajiya, mashin ɗin hawa bajaj mai lambar rijista Ondo QC 778, da sauransu.

Mr. Aya yace za'a gurfanar da mutanen gaban kotu da zarar hukumar ta gama gudanar da bincike.

A wani.labarin kuma IPOB Sun Sake Kai Sabon Hari Caji Ofis, Yan Sanda Sun Sheƙe 4 Daga Cikinsu

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan IPOB ne sun sake kai sabon hari caji ofis ɗin yan sanda a jihar Imo, kmar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Bala Elkana, shine ya tabbatar da haka, yace jami'an dake bakin aiki sun kashe huɗu daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel